Kwanan nan gwamna Matawalle zai shigo APC - Tsohon Gwamna Yarima

Kwanan nan gwamna Matawalle zai shigo APC - Tsohon Gwamna Yarima

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai koma jam'iyyar APC nan ba da dadewa ba. Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma tsohon Sanata, Ahmed Sani Yarima ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da jaridar Daily Trust a gidansa da ke Abuja.

A yayin da aka tambayesa ko akwai wani shiri da Mawatalle ya ke yi, wanda ya haye karagar kujerar gwamnan a karkashin jam'iyyar PDP, na sauya sheka, sai Yarima ya ce "akwai yuwuwar ya koma jam'iyyar APC din."

Tsakanin 1999 da 2003, Matawalle ya yi kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar Zamfara, Kwamishina muhalli da karkara da kuma Kwamshinan matasa da wasanni.

A yayin da aka tambayesa tabbaci a kan shirin sauya shekar gwamnan, sai Yarima ya ce "Ina tunanin mun dade da yin wannan maganar kuma shirye-shirye sun kammala. Nan ba da dadewa ba zai sauya sheka."

Duk da wannan tabbacin daga bakin Yarima kuwa, 'yan jam'iyyar APC a jihar na ci gaba da tururuwar komawa jam'iyyar PDP wajen gwamna Matawallen.

Tsohon sanatan ya ce: "Wannan siyasa ce. Ba za ku gane me ke faruwa ba. Zai dai koma kawai amma bai san waye tare da shi ba. Amma yanzu zai koma kuma zai tantance su waye suke tare da shi."

Kwanan nan gwamna Matawalle zai shigo APC - Tsohon Gwamna Yarima
Kwanan nan gwamna Matawalle zai shigo APC - Tsohon Gwamna Yarima
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta

Babban mai ba da shawara ga gwamna Matawalle kan wayar da kai, yada labarai da sadarwa, Zailani Bappa, ya ce mutane dai na ta hasashe ne na yuwuwar sauya shekar uban gidansa amma babu wannan tsarin.

"Zan iya tabbatar muku da cewa babu wani zancen sauya shekar Gwamna Bello Matawalle. Hankalinsa ya dauku a kan abubuwa masu tarin muhimmanci. Wannan kawai wata hanya ce ta dauke hankalinsa"In ji shi.

"Amma mun sani, bamu isa mu hana jama'a bayyana ra'ayinsu ba. Koda akwai wannan niyyar, zamu sanar da jama'a. Amma Gwamna Bello Matawalle ba shi da wannan burin na komawa APC." Bappa ya kara da cewa.

Matawalle ya wakilci mazabar Bakura/Maradun a 2003 a karkashin tsohuwar jam'iyyar ANPP. An sake zaben Matawalle a 2007 a karkashin jam'iyyar ANPP amma daga baya ya koma PDP inda aka zabesa a karo na uku a 2011.

Matawalle ya samu kuri'u 189,452 a zaben da aka yi na gwamnoni na watan Maris, 2019. Kotun koli ta kwace kujerar daga hannun Mukhtar Idris mai kuri'u 534,541 na jam'iyyar APC sakamakon rashin yin zaben fidda gwani.

Hakazalika, kotun koli ta jaddada hukuncin kotun daukaka karar wacce ta kwace kujera daga hannun dan takarar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel