CUPP: Burin takara tare da Bola Tinubu a APC ta sa Yakubu Dogara ya bar Jam’iyyar PDP
- Kungiyar CUPP ta fadi dalilin Rt. Hon. Yakubu Dogara na barin Jam’iyyar PDP
- CUPP ta ce tsohon Shugaban majalisar ya bar Jam’iyyar PDP ne saboda hangen 2023
- Ana jita-jitar Dogara zai fito takarar Shugaban kasa tare da Bola Tinubu a karkashin APC
Wata babbar kungiyar siyasa a Najeriya mai suna CUPP ta bayyana dalilin Yakubu Dogara na komawa jam’iyyar APC da ya bari kafin zaben 2019.
Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar ya fice daga jam’iyyar PDP ne a karshen makon nan, ya kuma koma APC mai mulkin kasa da rinjaye a majalisa.
Kungiyar CUPP ta yi magana game da lamarin, ta ce akwai yiwuwar jam’iyyar APC ta jawo Dogara ne domin ta cin ma manufar furofagandar addini a zaben 2023.
A cewar “Coalition of United Political Parties”, an yi wa Dogara tayin takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam’iyyar APC, ganin cewa Kirista ne shi daga yankin Arewa.
CUPP ta yi wannan bayani ne ta bakin mai magana da yawunta, Mista Ikenga Imo Ugo¬chinyere a jiya ranar Asabar, 25 ga watan Yuli 2020.
KU KARANTA: Ba mu san da labarin sauya-shekar Dogara ba - PDP
“Ina fatan ba ayi amfani da furofagandar fito da Kiristan Arewa a matsayin abokin takarar Bola Tinubu wajen janye aminina zuwa jam’iyyar APC da watakila ba za ta kai zuwa zaben 2023 ba.”
Uogchinyere ya ce game da siyasar Bauchi; “Gwamnan Bauchi na PDP bai kyautawa Dogara ba, ya yi watsi da shi duk da cewa shi ne ya yi ruwa da tsaki da kuri’un Tafawa-Balewa (a 2019)”
“Amma komawa jam’iyyar APC da ta ke da shugaba mai rauni wanda yanzu ya ke rasa martaba a idanun ‘yan jam’iyyar siyasa zai kawowa siyasar Yakubu Dogara cikas.”
Imo Ugochinyere ya kare da cewa: “Za mu ga yadda abubuwan nan duk za su kasance.”
Sauya-shekar da ‘dan majalisar mai wakiltar Bagora da Dass ya yi ya ba mutane da-dama mamaki, wannan shi ne karo na uku da ya canza jam’iyya daga 2014 zuwa yanzu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng