Dalilin da yasa na koma jam'iyyar APC — Gemade

Dalilin da yasa na koma jam'iyyar APC — Gemade

Tsohon shugaban jamiyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) na kasa, Senator Barnabas Gemade, ya bayar da dalilan da yasa ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gemade, wanda ya dawo jam'iyyar APC a karshen mako ya fice daga jam'iyyar ne a shekarar 2019 domin ya yi takarar kujerar sanata a karkashin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Makurdi, tsohon dan majalisar tarayyar da ya wakilci Arewa maso gabashin Makurdi ya ce komawarsa APC za ta taimakawa jam'iyyar lashe zabukanta da ke tafe nan gaba.

Dalilin da yasa na koma jamiyyar APC — Gemade
Dalilin da yasa na koma jamiyyar APC — Gemade
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yi sulhu tsakanin Bafarawa da Wamakko

"Maganar gaskiya ita ce a siyasa dole ka rika bin abinda zai taimaka maka cimma burinka. Lokacin da na bar PDP a 2015, ko 2014, na yi haka ne domin jam'iyyar ta dauki wasu matakai da za su hana ni cimma buri na na yin tazarce a matsayin sanata.

"Sai na ce, idan kana kallo ana kokarin dakile ka kuma ka tsaya toh ba ka da wayo. Hakan yasa ba bar APC a kan lokaci, kuma kamar yadda ka sani gwamnan yanzu ya yi takara da ni ya sha kaye.

"A 2019, an nemi hana ni takarar komawa majalisar dattawar ni kuma na sake sauya sheka zuwa wata jam'iyyar domin in cimma buri na."

"Ka san cewa a Benue tun 1999 a mazabu biyu mutanen da ke wakiltar jihar ba su canja ba, a Zone C, David Mark ya yi sanata sau biyar.

"A zone B, Sanata George Akuma yana neman komawa karo na hudu saboda ya riga ya yi waadi uku.

"Ni kuma ina kokarin koma wa karo na uku a zone A amma kwatsam kawai sai wasu suka ce wai lokacin su ne duk da cewa ba haka aka saba a sauran mazabun ba.

"Ni kuma da na lura ba dole ayi min adalci a APC wurin tsayar da dan takara ba sai na fice na koma SDP amma na makara domin ba mu samu lokacin shiri sosai ba balantana mu ci zabe.

"Tun daga wannan lokacin lamura sun canja a jihar mu. Hakan yasa na ga cewa ba zan iya samar da shugabanci mai nagarta da wakilcin da ya dace ba idan na tsaya a SDP.

"Hakan yasa na koma jamiyyar da na shiga a 2015 kuma muka samu babban nasara. Wannan shine dalilin da yasa na dawo APC," in ji Gemade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel