Dave Umahi: Kungiyar AESID ta roki ‘Yan Majalisar dokoki su sauke Gwamna
- Kungiyar mutanen jihar Ebonyi da ke ci-rani ta taso Gwamna Dave Umahi a gaba
- Wannan kungiya ta na so ‘Yan Majalisar jiha su tsige Gwamnan tun da ya bar PDP
- AESID ta ce doka ta bada dama gwamna ya canza jam’iyya ne idan rikici ya bijiro
Wata kungiya ta mutanen jihar Ebonyi da ke zaune a kasashen ketare sun roki majalisar dokoki ta fara kokarin ganin ta tunbuke David Umahi daga kan mulki.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, wannan kira ya zo ne bayan mai girma gwamnan ya fice daga jam’iyyar PDP, ya sauya-sheka zuwa APC mai mulki.
Kungiyar ta ce akwai hukuncin kotun koli da ya ce gwamna ba zai iya canza sheka ba har sai rikicin cikin-gida ya barke a jam’iyyarsa ko an samu rabuwar kai.
KU KARANTA: Gwamna Umahi ya sallami wasu Hadimansa bayan ya koma APC
Shugaban wannan kungiya ta AESID, Paschal Oluchukwu, ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, 2020, ya na neman a tunbuke gwamnan jiharsa.
Ambasada Paschal Oluchukwu ya ce tun bayan sauke Ali Modu Sheriff, babu wata rigima da ta bijiro a jam’iyyar PDP da har za ta sa Dave Umahi ya sauya-sheka.
A dalilin abin da AESID ta kira keta hakkin mutanen jiha, an roki ‘yan majalisar dokokin Ebonyi su yi maza-maza su fara aikin tsige gwamna Dave Umahi daga ofis.
Jawabin AESID ya ce: “Mun yi wannan kira ne saboda fahimtarmu na cewa Umahi (a matsayinsa na mutum) mai kokarin salwantar da jiharmu saboda manufarsa.”
KU KARANTA: Buhari ya yabi Umahi bayan ya sauya-sheka
“A karshe, kamar yadda mu ka saba nanata wa, jihar Ebonyi, ta mu ce gaba daya, burin wani mutum shi kadai, ba zai iya sa ayi watsi da nufin iyayenmu ba.”
Oluchukwu ya ce: “Ebonyi ba za ta kama da wuta ba saboda Umahi ya na so ya kare tuwonsa.”
Kwanaki baya kun ji cewa manyan jam’iyyar APC suna neman raba wasu Gwamnonin Jihohin adawa da PDP bayan sun yi nasarar sa Dave Umahi ya sauya-sheka.
Ana rade-radin APC ta na zawarcin Gwamnonin jihohin Bauchi, Enugu da kuma Kuros-Riba. Tuni gwamna Bala Mohammed ya yi maza,, ya musana rade-radin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng