Rashin adalcin PDP yasa na yi watsi da ita, Sanata Elisha Abbo

Rashin adalcin PDP yasa na yi watsi da ita, Sanata Elisha Abbo

- Sanata Ishaku Abbo na jihar Adamawa ya canja sheka, daga PDP zuwa APC

- A cewarsa, da a cikin duhu yake, amma canja shekarsa yanzu ya koma haske

- Ya kara da cewa, ya koma jam'iyyar APC ne saboda jam'iyyar adalci ce

Sanata Ishaku Abbo, mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana canja shekarsa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce ya bar jam'iyyar PDP ne don kowa ya san shi.

Legit.ng ta tattaro bayanan yadda dan majalisar da aka zaba a jam'iyyar PDP ya koma APC a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba.

Sai da sanatan suka yi wani taro da shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni, a babban ofishin jam'iyyar a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba a Abuja.

KU KARANTA: Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci

Rashin adalcin PDP yasa na yi watsi da ita, Sanata Elisha Abbo
Rashin adalcin PDP yasa na yi watsi da ita, Sanata Elisha Abbo. Hoto daga @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Inda Abbo ya sanar da manema labarai cewa ya bar jam'iyyar PDP ne saboda zalunci. Sannan ya bar duhu ya koma haske. A cewarsa, babban dalilin shiga siyasa shine yi wa al'umma aiki da taimakon talakawa da yi musu adalci.

"Ina son jam'iyyar APC saboda ta adalai ce. Da izinin Ubangiji jihar Adamawa za ta bunkasa a 2023, kuma za ta samu zabi na kwarai," yace.

KU KARANTA: Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, majalisar tarayya ta umarci kwamitin sadarwa da ta gayyaci ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami, don ta fahimtar dashi bukatar samar da mafita a kan tsaro ta ma'aikatarsa.

Kamar yadda takardar ranar Laraba tazo, wacce Ezrel Tabiowo, mai bayar da shawara na musamman ga shugaban majalisar tarayya a kan yada labarai yace, an yanke wannan shawarar ne saboda ganin halin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel