Interpol ta kama wasu ‘Yan Najeriya da ake zargi da laifin damfarar Kamfanoni

Interpol ta kama wasu ‘Yan Najeriya da ake zargi da laifin damfarar Kamfanoni

- Jami’an tsaro sun yi dace sun kama wasu kasurguman ‘Yan damfara a Najeriya

- Wadannan ‘Yan damfara sunyi wa kamfanoni da gwamnati lahani a kasashe 150

- Interpol ta hada-kai ne da ‘Yan Sandan Najeriya wajen cafke wadannan miyagu

Kungiyar ‘yan sanda ta Duniya ta damke wasu mutanen Najeriya uku bisa zarginsu da ake yi da hannu wajen tafka damfara da zamba cikin aminci.

Punch ta ce ana zargin wadannan mutanen ne da shiga ko ka hari a kan kamfanonin ‘yan kasuwa da gwamnatoci a cikin kasashe fiye da 150.

Akwai yiwuwar cewa mutanen nan ‘Yan Najeriya da ake zargi sun tafka ta’asa ta hanyar yi wa kamfanoni da hukumomi kutse ta shafukan yanar gizo.

KU KARANTA: Wani yaro ya hallaka mai gidansa a Najeriya

Jawabin da Interpol ta fitar a shafinta a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2020, ya bayyana cewa an kama wannan mutane a wani hari da aka kai.

Dakarun ‘yan sandan Najeriya da dakarun Group-IB na Interpol ne su kayi wani aiki da su ka yi wa lakabi da ‘Operation Falcon’, suka kamo mutanen uku.

Da ta ke bayani a kan yadda wadannan shu’umai suke damfafar jama’a, Interpol tace suna aika sakon Email na bogi ne da ya kan zama tarko a yanar gizo.

Wadannan mutane da ake zargi su kan shiga rigar ‘yan kasuwa suna yaudarar masu cefane, ko su labe da sunan tallafin COVID-19 ko dabarar tallar kaya.

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa wani Matashi dauri a gidan yari saboda laifin damfara

Interpol ta kama wasu ‘Yan Najeriya da ake zargi da laifin damfarar Kamfanoni
Interpol Hoto: www.journalofdemocracy.org/articles/weaponizing-interpol
Source: UGC

Ta haka ne ake tura wa mutane samfarorin manhajojin cuta zuwa cikin na’urorinsu ko shafinsu.

Interpol ta ce AgentTesla, Loki, Azorult, Spartan, da Trojans suna cikin abubuwan da wadannan miyagu suke jefa wa wadanda su ka shiga cikin tarkon na su.

A jiya tsohon shugaban binciken harkar fansho, Abdulrashid Maina yace yana kokarin kawo gyara amma miyagu sun yi masa shamaki da shugaban kasa.

Maina ya ce zai tona asirin yadda wasu jami'an EFCC su ka ci-hanci, suka saki marasa gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel