Kotu ta yi wa wani ɗaurin shekaru 125 a Maiduguri saboda satar N12m

Kotu ta yi wa wani ɗaurin shekaru 125 a Maiduguri saboda satar N12m

- Kotu ta yanke wa wani Allen Abel hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru 125 bayan samunsa da laifin satar kudi kimanin Naira miliyan 12

- Alen da wasu mutum biyu sun hada baki ne sun yaudari wasu kamfanoni sun karbi taliya da buhanan shinkafa da kudinsu ya haura Naira miliyan 12 da sunan kwangilar ciyar da yara 'yan makaranta na gwamnati

- Hukumar EFCC ta gurfanar da Abel da sauran mutanen biyu kan laifuka 20 kuma kotu ta same su da laifi da yanke musu hukunci

Wata babban kotun jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri ta yanke wa wani Allen Abel hukuncin zaman gidan yari na shekaru 125 saboda damfarar da ya yi wurin karbar kayan abinci da kudinsu ya kai N12, 879,800.00.

Kotu ta yi wa wani daurin shekaru 124 a gidan gyaran hali
Kotu ta yi wa wani daurin shekaru 124 a gidan gyaran hali. Hoto: @Lindaikeji/@Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Abel ya yi wannan damfarar ne da sunan zai yi wa gwamnatin tarayya kwangila a karkashin shirin ciyar da yara 'yan makaranta da ke ma'aikatar jin kai da kare afkuwar bala'i na kasa.

Wannan na cikin wata sanarwa ce da shugaban sashin watsa labarai da hulda da jama'a na hukumar yaki da rashawa, Mista Wilson Uwujuren ya fitar.

Sanarwar ta ce hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Abel a gaban Mai shari'a Aisha Kumaliya a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020 tare da Suleiman Adamu, Usman Adamu da Kingsley Madubuagu kan laifuka 20 masu alaka da yaudara, sojan gona, gabatar da takardun bogi.

Tuhuma da uku da aka yi masa ta ce: "A wani lokaci tsakanin watannin Fabrairu da Maris din 2020 a Maiduguri jihar Borno, kai Allen Abel da Suleiman Adamu da Usman Adamu kun karbi katon na taliya 1313 da buhunan shinkafa 480 da kudinsu ya kai N12, 110,000.00 daga hannun wata Lelle Hyelwa Sini na kamfanin Lelle Foreaight Construction Co. Ltd da sunan za kuyi kwangilar samar da kayan abinci da ma'aikatar jin kai da kare bala'i (karkashin shirin ciyar da 'yan makaranta na gwamnati) duk da kun san karya ku ke yi wadda hakan laifi ne da ya ci karo da doka."

KU KARANTA: Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja

Abel ya amsa dukkan laifukan 20 da aka tuhume shi da aikatawa kuma mai shari'a Kumaliya ta same shi da laifi da dage zaman zuwa ranar 30 ga watan Satumba don yanke hukunci.

A ranar Laraba 30 ga watan Satumban 2020, Mai shari'a Kumaliya ta yanke wa Abel shekaru 7 a kan kowanne laifuka daga na 1 zuwa 7 da na 9 ba tare da zabin biyan tara ba. Shekaru biyar a kan kowanne laifi na 7, 8 da kuma 11 zuwa 20 ba tare da zabin biyan tara ba.

Za a zartar da hukuncin ne dukkansu a lokaci guda.

Har wa yau, wanda aka yanke wa laifin zai biya kamfanin Lele Foresight Construction Company kudi N12, 110,000.00 sannan ya biya HIE Global Investment Limited kudi N769,800.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164