Ta lalama ba barazana ba Ibo za su samu shugabanci inji Hope Uzodinma

Ta lalama ba barazana ba Ibo za su samu shugabanci inji Hope Uzodinma

- Dole Ibo su yi amfani da siyasa wajen cin ma burin shugabanci a 2023

- Sanata Hope Uzodinma ya yi gargadi game da tada rikici da barazana

- Gwamnan na Imo ya yabi mai neman zama sabon shugaban Ohanaeze

Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya shiga cikin ‘yan siyasar da su ke tofa albarkacin bakinsu game da zabe mai zuwa na 2023, tun yanzu.

Mai girma gwamna Hope Uzodimma ya ce da lalama Ibo za su karbi mulkin Najeriya, ja-kunne cewa barazana da neman tada rigima ba za suyi aiki ba.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da aka kaddamar masa da sabon ‘dan takarar shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor.

KU KARANTA: Kungiya ta tsaida Yari ya karbi shugabancin APC bayan Oshiomhole

A ra’ayin Uzodinma, Farfesa George Obiozor ya cancanci rike shugabancin kungiyar Inyamuran.

Da ya ke jawabi ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba, a garin Owerri, jihar Imo, Hope Uzodimma ya bayyana nasarorin da Ibo suke samu a fadin kasar nan.

Uzodimma ya ce a yau mutanen Ibo suna rike shugabanci a gidan soja, aikin gwamnati, da bankuna, duk a dalilin kokarin Marigayi Dr. Nnamdi Azikwe.

Gwamnan ya ja-kunnen masu buga tamburan rigingimu, ya ce ta hanyar tattauna wa ne kurum Ibo za su kai ga mulkin Najeriya ba yunkurin fito-na-fito ba.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Imo yana yi wa APC zawarcin Gwamnonin PDP

Ta lalama ba barazana ba Ibo za su samu shugabanci inji Hope Uzodinma
Hope Uzodinma Hoto: twitter.com/govhopeuzodinma
Asali: Facebook

Sanata Uzodimma ya tabo maganar fafutukar samar da kasar Biyafara mai ‘yancin kanta, ya ce mutanen Najeriya sun san Ibo suna neman shugabanci a yau.

A halin yanzu APC tana cigaba da ratsa yankin Kudu maso gabas, har ya kai tana da gwamnoni biyu sakamakon sauyin-shekar da gwamnan Ebonyi ya yi.

Tunde Fashola ya bukaci shugabannin APC da 'yan siyasa su cika alkawarin da aka yi a 2015, a bar a bar mutanen Kudu su karbi shugabancin Najeriya a 2023.

Yankin da za su fito da magajin shugaba Buhari zai fito yana gwara kan jiga-jigan APC mai mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng