Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma

Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma

- Gwamna Uzodinma, ya ce yana da tabbacin David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, zai koma APC

- Gwamnan jihar Imo yana bai wa gwamnonin PDP shawara a kan komawa jam'iyya mai ci

- Uzodinma ya shawarci mutanen yamma maso gabas, da su mara wa jam'iyyar APC baya

Gwamna Hope Uzodinma ya ce bayan David Umahi ya koma jam'iyyar APC, gwamnoni da dama za su yi ta tururuwar shiga jam'iyyar.

Gwamnan jihar Imo ya fadi hakan ne a wata takarda ta ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, bayan ya ziyarci babban ofishin APC da yake Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Uzodinma ya ce kwanan nan gwamnoni PDP za su yi ta komawa APC.

A cewarsa: "Yau ina matukar farinciki sanar da ku cewa saura sa'o'i kadan, jagora kuma jagaban al'umma, gwamnan jihar Ebonyi, zai koma APC.

"Hakika ina matukar farin cikin komawarsa jam'iyyarmu, kuma ina mai tabbatar muku, gwamnoni da dama za su cigaba da komawa."

Ya ce yana da matukar muhimmanci a ce mutanen kudu maso gabas sun shiga APC don a dama da su.

KU KARANTA: Bidiyon dan sanda ya ki karbar cin hanci, yana jan kunnen direban a kan bashi da yayi

Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma
Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma. Hoto daga @GovtOfImoState
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga kauyen Kaduna, sun kwashe mutum 11

A wani labari na daban, Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel