Gwamna Wike ya maida martani ga Umahi kan zargin PDP da rashin adalci

Gwamna Wike ya maida martani ga Umahi kan zargin PDP da rashin adalci

- Gwamna Nyesom Wike ya yi wa Dave Umahi raddi bayan ya fice daga PDP

- Wike ya ce dama alamu sun nuna Gwamnan na Ebonyi zai shiga tafiyar APC

- A cewar Wike, Gwamna Umahi ya na neman mulki ne kawai ba wani abu ba

A ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tofa albarkacin bakinsa game da sauyin-shekar Dave Umahi.

Gwamna Nyesom Wike ya ce Dave Umahi ya bar jam’iyyar PDP ne domin ya samu kai wa burinsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Nyesom Wike ya yi maza ya fitar da jawabi ta bakin wani mai taimaka masa wajen harkar yada labarai, Kelvin Ebiri, inda ya yi wa Dave Umahi raddi.

KU KARANTA: Gwamnonin Jihohin da su ka tsere daga Jam’iyyarsu tsakanin 2019 - yau

Ta bakin Mista Ebiri, gwamnan Ribas ya ce jam’iyyar adawar ba ta zalunci yankin Kudu maso gabas ba domin Ibo sun rike mukamai a gwamnatin PDP.

Wike ya ke cewa barin jam’iyyar PDP da gwamna Umahi ya yi, bai zo wa duk wani cikakken ‘dan jam’iyyar da mamaki ba, domin kuwa sun san dama a rina.

A cewar gwamna Wike, takwaran na sa na jihar Ebonyi, ya dade yana hulda da jam’iyyar APC.

“Abokina Umahi ya na so ya zama shugaban kasa, babu matsala a kan wannan. Ka na da damar neman zama shugaban kasa, babu wanda ya isa ya hana ka.”

KU KARANTA: Abin da ya sa Umahi ya juya mana baya - PDP

Gwamna Wike ya maida martani ga Umahi kan zargin PDP da rashin adalci
Nyesom Wike Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

“Ka na da ilmi. Ka rike gwamna har sau biyu, saboda haka ka cancanci ka ce kana son zama shugaban kasa.” Gwamna Wike a jawabin na sa na jiya.

“Martani na ga Umahi shi ne, ya na da damar sauya-sheka, amma ya ce ya canza jam’iyya saboda zaluncin da ake yi wa Kudu ta gabas, wannan cin fuska ne.”

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan na jihar Ebonyi ya alakanta komawarsa APC da cewa jam’iyyar za ta kare muradun mutanen kudu maso gabas.

Umahi ya shiga sahun gwamnoni hudu da su ka tsere daga Jam’iyyarsu bayan sun lashe zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel