Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi

Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi

- Daga karshe, gwamnan Ebonyi ya alanta fitarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC

- Gwamna Umahi ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar fita daga PDP

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ba ya nadamar sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga Peoples Democratic Party PDP.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a birnin Abakaliki yayinda yake hira da manema labarai kan cece-kucen da sauya shekarsa ta haifar, rahoton The Nation.

Gwamnan ya ce ya koma APC ne saboda rashin adalcin da jam'iyyar PDP take yiwa yankin kudu masi gabas.

Hakazalika ya bayyana cewa bai yi wani yarjejeniya da APC kan baiwa yankin kujerar shugabancin kasa a 2023 ba.

KU KARANTA: Bayan komawar Umahi APC, ga jerin gwamnonin PDP da za su biyo shi, Uzodinma

Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi
Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin Gwamnonin Najeriya masu-ci da su ka fice, su ka canza Jam'iyya

Kungiyar yan kabilar Igbo a gida da waje, Ohanaeze Ndigbo, ta amince da sauya shekar da gwamnan Ebonyi, David Umahi, daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress APC.

An ruwaito cewa Umahi ya bayyanawa jagororin uwar jam'iyyar PDP a wata ganawa a Abuja, ranar Talata, cewa yana son fita daga jam'iyyar ne saboda an ki baiwa yankin Igbo kujerar shugabancin kasa a 2023.

Mataimakin Kakakin Ohanaeze, Cif Chuks Ibegbu, ya siffanta sauya shekar Umahi matsayin aikin kwarai.

Ibegbu ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch a Enugu ranar Laraba.

Ya ce PDP za ta yi rashin hallaci idan bata baiwa yankin Igbo kujerar takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng