Jerin Gwamnonin Najeriya masu-ci da su ka fice, su ka canza Jam'iyya

Jerin Gwamnonin Najeriya masu-ci da su ka fice, su ka canza Jam'iyya

- Mun tattaro duk Gwamnonin Jihohin Najeriya masu-ci da su ka sauya-sheka

- Daga 2015 zuwa yanzu, an samu gwamnoni hudu da su ka bar jam’iyyarsu

- Gwamnan da ya sauya-shekan a karshe shi ne Dave Umahi na jihar Ebonyi

Sauyin-sheka ya na cikin tarbiyyar ‘yan siyasa musamman a Najeriya. Daga cikin gwamnonin da su ka dare karagar mulki, akwai wadanda su ka canza jam’iyya.

Kamar an hada-baki, biyu daga cikin gwamnonin sun fice ne daga jam’iyyar PDP zuwa APC, yayin da su kuma ragowar sun rungumi PDP bayan barin tafiyar APC.

Biyu daga cikin wadannan gwamnoni sun fito ne daga Kudancin Najeriya, ragowar biyun sun fito ne daga yankin Arewa. Ga dai cikakken jerin gwamnonin hudu:

KU KARANTA: Buhari na bukatar goyon - baya inji Tambuwal

1. Samuel Ortom

Samuel Ioraer Ortom ya na cikin wadanda su ka kaurace wa jam’iyyar APC ya koma PDP a 2018, gwamnan na Benuwai ya yi nasararar samun tazarce a karkashin PDP a zaben 2019.

Ba wannan ne karon farko da Gwamnan ya sauya-sheka ba, asali ma daga PDP ya shigo APC a 2015.

2. Aminu Waziri Tambuwal

Gabanin zaben 2019, gwamnan jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya rabu da jirgin APC duk da nasarar da jam’iyyar ta ba shi a 2015, ya koma jam’iyyar hamayya ta PDP.

Tambuwal ya nemi tikitin shugaban kasa a PDP, da ya gaza nasara, ya koma takarar gwamna.

KU KARANTA: Buhari da Gwamnoni sun ba Jama’a kunya – Kungiyoyin Arewa

Jerin Gwamnonin Najeriya masu-ci da su ka fice, su ka canza Jam'iyya
Dave Umahi Hoto: Thecable.ng
Asali: UGC

3. Godwin Obaseki

Wani gwamna mai-ci da ya sauya-sheka shi ne Godwin Nogheghase Obaseki. Gwamnan na Edo ya lashe zaben 2016 a karkashin APC, amma daga baya dole ta sa ya bi jam’iyyar adawa.

Obaseki ya koma PDP ne bayan rigimarsa da Adams Oshiomole ta sa ya rasa tikiti a APC.

4. David Umahi

Na karshe daga cikin jerin na mu shi ne gwamnan jihar Ebonyi, David Nweze Umahi, wanda ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa jam’iyyar APC a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2020.

Gwamnan ya rabu da jam’iyyarsa a sakamakon abin da ya kira rashin adalcin da ake yi wa yankinsa.

Da ya ke jawabi dazu, gwamnan na Ebonyi, ya ce sam bai yi nadamar barin jam'iyyar PDP ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel