Da sannu, 'yan Najeriya za su san dalilin da yasa Umahi ya koma APC, PDP

Da sannu, 'yan Najeriya za su san dalilin da yasa Umahi ya koma APC, PDP

- Dave Umahi ya kawo karshen labarin ficewa daga PDP inda ya bayyana komawa APC ranar Talata

- Babu wanda yafi karfin jam'iyyar PDP, Umahi ya fita ne bisa radin kansa

- Umahi na ganin cewa jam'iyyar APC zata bawa dan yankin kudu maso gabas takarar shugaban kasa a 2023 dalilin da yasa ya tsallako daga PDP kenan

Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce 'yan Najeriya "za su san dalilin fitar Gwamna Dave Umahi daga jam'iyyar in lokaci ya yi".

Ologbondiyan, wanda ya bayyana haka da yammacin Talata a shafinsa na Twitter, "jam'iyyar PDP ta ce gwamnan Ebonyi, Engr. Dave Umahi ya bar jam'iyyar saboda dalilan sa, wanda 'yan Najeriya zasu sani in lokaci ya yi.

Da sannu, 'yan Najeriya za su san dalilin da yasa Umahi ya koma APC, PDP
Da sannu, 'yan Najeriya za su san dalilin da yasa Umahi ya koma APC, PDP. Hoto: PM News
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

"Jam'iyyar mu tana godiya ga Gwamna Umahi wanda ya yi aiki ga al'ummar Jihar Ebonyi, a matsayin shugaban jam'iyyar PDP a jihar (2003 - 2007), mataimakin gwamna (2007 - 2015) da kuma gwamna sau biyu (2015 har yanzu) duka a karkashin jam'iyyar PDP.

"A yayin da muke fatan alheri ga Umahi, muna kira ga ragowar 'yan PDP da su ci gaba da zama lafiya da kiyaye muradan jam'iyyar kasancewar ba wani mutum da yafi karfin PDP."

Umahi ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata, ya kawo karshen rahotannin da ke cewa ya bar jam'iyyar zuwa APC.

KU KARANTA: Rundunar Sojin Saman Najeriya ta karyata cewa Boko Haram ta harbo jirgi a Borno

Jaridar Punch a baya bayan nan ta rawaito Umahi ya gana da shugabannin jam'iyyar PDP kuma ya fada musu zai bar jam'iyyar don komawa APC.

Gwamnan ya shaidawa shugabannin PDP na kasa karkashin shugabanta na kasa Prince Uche Secondus cewa jam'iyyar APC zasu biya bukatarsa na bawa dan yankin kudu maso gabas takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164