Sarkin Saudiyya Salman ya yi wa kasar Iran wankin babban bargo

Sarkin Saudiyya Salman ya yi wa kasar Iran wankin babban bargo

- Sarki Salman na kasar Saudiyya ya caccaki kasar Iran a kan katsalandan da take yi wa kasashen da ke makwabtaka

- Sarki Salman ya bukaci daukar tsatsauran matakai domin tabbatar da ganin kasar ba ta samu muggan makamai na kare dangi ba

- Saudiyya dai ta amince da tsarin Shugaban kasar Amurka, na sanya matsin lamba ga Iran

Mai alfarma sarkin Saudiyya, Sarki Salman, ya yi wa kasar Iran wankin babban bargo yayinda ya bayyana cewa akwai bukatar daukar tsatsauran matakai domin tabbatar da ganin cewa kasar ba ta samu muggan makamai na kare dangi ba.

An tattaro cewa Sarki Salman na zargin Iran da yi wa kasashen da ke makwaftaka da ita katsalandan a harkokinsu.

A cewarsa hakan na janyo karuwarb matsalar ta’addanci da kuma hura wutar rikici da fargaba.

KU KARANTA KUMA: Dogarin Gwamna Obaseki ya yanke jiki ya fadi a wajen bikin rantsar da shi (bidiyo)

Sarkin Saudiyya Salman ya yi wa kasar Iran wankin babban bargo
Sarkin Saudiyya Salman ya yi wa kasar Iran wankin babban bargo Hoto: Time Magazine
Asali: UGC

Masana sun bayyana cewa kasar Saudiyya ta amince da tsarin Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, domin matsin lamba ga Iran, wanda ciki har da saka takunkumi da zai shafi tattalin arziƙin kasar.

Sai dai ana zaton gwamnati mai jiran gado ta Mista Joe Biden za ta sassauta wa Iran din, Shashin Hausa na BBC ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye

A wani labarin, hukumar yan sanda dake Hague, kasar Netherlands a ranar Alhamis, 11 ga Nuwamba, ta tabbatar da labarin cewa an yi harbe-harbe a ofishin jakadancin kasar Saudiyya.

Bayan samun labarin harbe-harben, jami'an tsaron garin inda kotun duniya ICC take sun garzaya cikin ginin kuma sun samu harsasai a kasa, tashar ABC News ta ruwaito.

Amma, a cewar kakakin hukumar yan sanda dake Hague, Steven van Santen, babu wanda aka kashe ko ya ji rauni.

Har yanzu, yan sanda basu san dalilin da yasa aka kai hari ofishin jakadancin Saudiyya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng