Dogarin Gwamna Obaseki ya yanke jiki ya fadi a wajen bikin rantsar da shi (bidiyo)
- Dogarin Gwamna Godwin Obaseki ya yanke jiki ya fadi a yayin rantsar da gwamnan a karo na biyu
- Lamarin ya afku ne a yau Alhamis, 12 ga watan Oktoba, lokacin da gwamnan ke jawabin rantsar da shi
- Sai dai wasu jami'an DSS sun yi nasarar bashi taimako cikin nutsuwa yayinda aka garzaya da shi asibiti
Dogarin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, ya yanke jiki ya fadi a yayin bikin rantsar da gwamnan a karo na biyu a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke jihar.
Sanye cikin kayan aiki, an gano dogarin wanda ya tsaya a bayan gwamnan da aka rantsar ya koma baya ya jingina kafin ya fadi, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
An tattaro cewa gwamnan na tsaka da karanto jawabin rantsar dashi a lokacin da al’amarin ya afku.
KU KARANTA KUMA: Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye
Yayin da jami’in dan sandan ya fadi, wasu jami’an tsaro na farin kaya (DSS) su biyu sun isa wajen cikin nutsuwa domin ceto shi sannan suka raka shi wajen da aka tanada don zama.
A daidai wannan lokacin sai kwamishinan lafiya na jihar, Dr Patrick Okundia, ya yi gaggawan zuwa don duba jami’in tare da daidaita shi.
An kuma tattaro cewa an yi gaggawan daukarsa zuwa cikin motar asibitin da aka girke a filin wasan sannan aka yi asibiti da shi.
Taron wanda ya gudana a filin wasa na Samuel Ogbemudia an yi shi ne a saukake, sannan babban alkalin jihar, Hon. Justice Esther Edigin ya jagoranci rantsar da gwamnan.
KU KARANTA KUMA: An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa
Mataimakin gwamnan, Philip Shaibu, ne ya fara karbar rantsuwar kama aiki bisa rakiyar uwargidarsa da misalin karfe 11:48 na safe kafin Gwaman Godwin Obaseki ya karbi nasa rantsuwar bisa rakiyar matarsa da karfe 12:00 na rana.
Ga bidiyon a kasa:
A gefe guda, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo ya kwatanta kansa a matsayin sabuwar ma'anar demokradiyya, The Cable ta wallafa.
Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ake rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu, wanda aka yi a Samuel Ogbemudia a Benin, babban birnin jihar Edo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng