Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye

Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye

- Yan sanda sun kama wani saurayi bisa zargin kashe budurwarsa da kuma binne ta

- An tattaro cewa an kai rahoton batan matashiyar a ofishin yan sanda a yankin Lekki da ke Lagas inda suka bazama bincike

- Gani na karshe da aka yi wa marigayiyar shine lokacin da saurayin ya nemi ta kawo masa ziyara gidansa

Rundunar yan sandan Lagas ta kama wani dan shekara 29, Segun Titilayo, na garin Otolu, karamar hukumar Lekki da ke jihar bisa zargin kashewa da kuma birne budurwarsa mai suna Oritoke Manni, mai shekaru 26.

Tuni dai dama rundunar yan sanda ta kaddamar da batan Manni wacce ta kasance mai aiki a wata mashaya ta otel din K.C, garin Apakin da ke Lekki.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya ce a ranar 13 ga watan Oktoba da misalin karfe 11 na safe, wanda ake zargin, Segun Titilayo ya kira marigayiyar inda ya bukaci ta kawo masa ziyara a gidansa.

Wannan shine ganin karshe da kowa ya yi wa Oritoke a raye.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: IGP ya buƙaci N24.8bn domin sayen fetur wa motoci da baburan ƴan sanda

Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye
Yadda saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya binne ta a boye Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

“Rundunar yan sanda ta samu rahoto kan lamarin batan marigayiyar. An baza batun batan nata a dukkanin ofishoshin yan sanda a fadin jihar domin bincike da daukar matakin da ya kamata.

"Sai dai kuma, a ranar 7 ga watan Nuwamban 2020, wani Injiniya Adegbago David, na kamfanin Adron Homes and Properties, ya shigar da rahoto ofishin yan sandan Akodo, jihar Lagas, cewa yayinda kamfanin ke aikin hake-hake a garin Otolu, motar katafilarsu ta hako gawa.

"Sai jami’an yan sandan suka shiga aiki sannan aka gano cewa gawar na Oritoke ne. Sai aka kwashe gawar zuwa wani wajen ajiyar gawawwaki domin yin gwaji.

“Yan sandan sun shiga farautar wanda ake zargin sannan aka kama shi. An tsare shi a sashin SCID Panti sannan yana bayar da jawaban da za su taimaka wa yan sanda a bincikensu,” in ji shi.

A cewar kakakin yan sandan, kwamishinan yan sandan jihar, CP Hakeem Odumosu, ya yi Allah-wadai da aika-aikan, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci

Ya kuma umurci mataimakin CP da ke kula da sashin CID na jihar, DCP Yetunde Longe, da ya gudanar da bincike sosai a kan lamarin.

A wani labarin, Rundunar yan sanda ta kama wani malami bisa laifin garkuwa da wani tsohon dalibinsa mai shekaru takwas a yankin Akute da ke jihar Ogun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng