Tattalin arziki: Dalar Amurka ta na N460, gangar mai ya kai fam $40

Tattalin arziki: Dalar Amurka ta na N460, gangar mai ya kai fam $40

- Farashin gangar danyen mai a kasuwar Duniya ya kai fam $40.5

- Kimar Naira ta na kara yin kasa a kan Dala a kasuwar ‘yan canji

- Kudin kasar wajen Najeriya zai isa watanni takawas ana sayayya

Darajar Naira ta karu da sama da kashi 2% a farkon makon nan. Hakan na zuwa be bayan annobar da ta barke a wasu bangarorin kasar Amurka.

A halin yanzu tattalin arzikin kasashe ya na tangal-tangal sakamakon annobar cutar COVID-19. Masana sun ce za a dauki lokacin kafin a farfado.

Rahoton ya ce rufe wasu matatu da aka yi a yankin yammacin jihar Alabama ya taimaka wajen tashin farashin danyen man a kasuwannin Duniya.

KU KARANTA: Naira ta karye raga-raga a kasuwar canji

Wani babban jami’in kamfanin Rystad Energy, Bjornar Tonhaugen ya ce yanayin da aka shiga a Amurka ya taimakawa kasuwar danyen mai sosai.

Gangar danyen man ‘Brent’ ya karu da 2.3% inda yanzu kudinsa ya koma $40.53. An yi wa gangar ‘West Texas’ kudi a kan $38.28 a ranar Talatar nan.

Tattalin arziki: Dalar Amurka ta na N460, gangar mai ya kai fam $40
Farashin danyen mai ya na juya kudin fetur a Najeriya
Asali: Twitter

Darajar danyen man West Texas ya karu da kusan fam $1 kamar yadda Reuters ta bayyana jiya.

Masu hasashe su na ganin cewa farashin man zai karye a ragowar wannan shekara. Irinsu IEA sun bayyana wannan a rahoton wata-wata da su ka fitar.

KU KARANTA: Gwamnati za ta rage karfin giyar da ake saidawa a rabobi

A gida Najeriya kuma labarin bai da dadin ji sosai domin kuwa an saida Dalar Amurka a kan N460 a kasuwar canji a ranar Talatar nan da ta gabata.

A baya kun ji cewa babban banki ya dawo wa da ‘yan canji Dala a kan farashi mai rahusa, duk da haka, darajar Naira ta fadi jiya bayan tashin makon jiya.

A ranar Alhamis, ‘yan canji sun saida Dalar Amurka a kan N440. Idan ba ku manta ba, kafin wannan lokaci an saye Dalar har a kan N480 kwanaki.

A jiyan ne kuma gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce akwai dala biliyan $36 a asusun kudin kasar wajen Najeriya, abin da zai isa kasar watanni takwas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel