Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno

Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno

- Rundunar yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa ba za ta bari ayi kowani irin zanga-zanga ba a jihar

- Kakakin rundunar, Edet Okon ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa

- Okon ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan Borno ya yi umurnin cewa kada a bari a gudanar da zanga-zanga

Rundunar yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa ba za ta bari ayi kowani irin zanga-zanga ko gangamin jama’a ba kan daga farashin man fetur da na wutar lantarki da aka yi.

Kakakin rundunar, Edet Okon a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, ya ce har yanzu akwai haramci kan gangamin jama’a a jihar, jaridar This Day ta ruwaito.

Ya ce yan sandan na sane da shirin da wasu mutane ke yi na gudanar da zanga-zangar tashin hankali a jihar da sunan nuna ra’ayinsu kan karin kudin man fetur da na wutar lantarki da sauransu.

Kakakin ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan Borno, Mohammed Ndatsu Aliyu ya yi umurnin cewa kada a bari a gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihar.

KU KARANTA KUMA: An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno
Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno Hoto: Getty Images
Asali: UGC

A cewar jaridar Vanguard, Okon ya yi bayanin cewa an sanya haramci kan zanga-zanga ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro a jihar.

A wani labarin kuma, akwai alamu da ke nuna cewa Najeriya na iya fuskantar gagarumin zanga-zanga daga dalibai a kan karin farashin man fetur.

Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta bai wa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adi domin ta janye karin farashin man fetur ko kuma ta fuskanci gagarumin zanga-zanga daga dalibai, jaridar Leadership ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zargin Fyade: An shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa, Abdulmumuni Danga

Mataimakin Shugaban NANS, Ojo Raymond, ya bayyana cewa daliban Najeriya basu amince da karin ba.

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce gwamnati ba za ta mayar da tallafin kuɗin man fetur ba ma'ana janye tallafin ya zauna daram dam kenan.

Buhari ya kuma ce ƙarin kuɗin wutar lantarki da kamfanonin rabar da wutar lantarki, DisCos suka yi ya zama dole ne duk da cewa abin ya dame shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnati na iya ƙoƙarin ta domin rage raɗaɗin da ƙarin zai yi a rayuwar al'umma a lokaci guda kuma yana ƙoƙarin ceto tattalin arzikin ƙasar daga ruguje wa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel