Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC sun fara zawarcin kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa baki daya, tare da wasu manyan mukamai na jam'iyyar kafin zaben.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu majiyoyi masu karfi daga babban ofishin jam'iyyar na kasa da ke Abuja, sun bayyana cewa ba a riga an saka ranar zaben shugabannin jam'iyyar ba.

Daya daga cikin 'yan takarar wanda ya tabbatar da cewa zai shiga jerin masu bukatar shugabancin jam'iyyar na kasa, ya kuma bukaci a boye sunansa, ya ce, "Zan bayyana wa jama'a burina nan ba da dadewa ba."

Jaridar Daily Trust ta tabbatar da cewa, daga cikin masu bukatar hayewa kujerar shugabancin jam'iyyar, akwai tsoffin gwamnonin jihohin Gombe da Cross River tare da wani tsohon kwamishinan Cross River.

A halin yanzu, suna tuntubar masu ruwa da tsaki kafin su bayyana burinsu ga jama'a karara.

Wasu manyan 'yan siyasa daga jihohin Buachi da Kaduna, sun tabbatar da cewa suna hangen wasu manyan matsayi a majalisar aiwatar da ayyuka na jam'iyyar.

A watan Yunin wannan shekarar ne majalisar zartarwa ta jam'iyyar APC (NEC), ta sauke dukkan masu mukami na majalisar aiwatar da ayyuka na kasa (NWC) na jam'iyyar APC.

Bayan nan, an kafa kwamitin rikon kwarya mai mambobi 13 don shugabantar jam'iyyar na rikon kwarya, wanda suka samu shugabancin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Daga cikin alhakin da aka daura wa kwamitin rikon kwaryar, akwai tabbatar da shirya gagarumin taron jam'iyyar a cikin watanni shida, wanda a nan za a zaba sabbin shugabannin jam'iyyar.

Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai
Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

KU KARANTA: Hotunan Tinkiya mafi tsada da aka taba siyarwa a duniya, an siyeta a N190m

A wani labari na daban, a cikin kokarin kwamitin sasanci na rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ya samu jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Litinin an yi nasarar sasanta ministan sufuri, Rotimi Amaechi da takwaransa, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva.

Dukkan ministocin sun amince za su yi aiki tare don kawo gyara a jam'iyyar a yankin kudu-kudun kasar nan. Amaechi ya taba yin gwamnan jihar Ribas, hakazalika Sylva ya taba zama gwamnan jihar Bayelsa.

A yayin bayanin wannan ci gaban ga manema labarai, bayan tattaunawar sirri da aka yi tsakanin tsoffin gwamnonin da shugaban kwamitin rikon kwaryar a babban ofishin jam'iyyar APC a Abuja, sun tabbatar da sasancin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel