Gamayyar kasashen nahiyar Afrika ta yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a Mali

Gamayyar kasashen nahiyar Afrika ta yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a Mali

Gamayyar kasashen nahiyar Afrika AU, ta yi Alla-wadai da damke shugaban kasan Mali, Ibrahim Keita da Firam Mininsta Boubou Cisse, da sojojin kasar sukayi

Legit ta kawo muku rahoto cewa wasu Sojoji a MaLi yau Talata sun damke shugaban kasa da wasu mamabobin majalisarsa a gidansa dake BamakO, babbar birnin kasar.

"Muna masu fada muku cewa shugaban kasa da Firam Minista na hannunmu" Daya daga cikin Sojin ya bayyanawa AFP.

Martani kan hakan, shugaban gamayyar kasashen Amfirka, Mousa Faki, ya yi kira ga sakin su biyu ba tare da bata lokaci ba.

Hakazalika ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin duniya su nuna rashin amincewarsaru da yunkurin amfani da karfin Soja wajen mulki a Mali.

Faki ya bayyana hakan ne a shafin na Tuwita.

Yace: "Ina mai Alla-wadai da damke shugaba Ibrahim Boubacar Keita, Friam Minista da sauran mambobin majalisar gwamnatin kasar Mali kuma ina kira ga a sakesu."

"Ina Alla-wadai da duk wani yunkurin canji da ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ina kira ga Sojojin su janye daga amfani da karfi kuma su girmama demokradiyya."

"Ina kiraga ECOWAS, majalisar dinkin duniya da dukkan kungiyoyin duniya su hada karfi da karfe wajen hana amfani da karfin soja wajen kawo karshen rikicin siyasa."

KU KARANTA: Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari

Gamayyar kasashen nahiyar Afrika ta yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a Mali
Gamayyar kasashen nahiyar Afrika ta yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a Mali
Asali: Depositphotos

Gabanin damke shugaban kasan a yau Talata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine wakilin ECOWAS da aka tura sulhunta rikicin Mali, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyanawa Buhari cewa kungiyar adawa a kasar Mali, M5, ta doge kan bakanta cewa sai shugaba Keita ya yi murabus

Za ku tuna cewa a watan Yuli, shugaba Buhari da wasu shugabannin ECOWAS sun kai ziyara kasar Mali domin sulhunta bangarori biyu amma ganawarsu da shugaban hamayya, Imam Dicko, ya kare a baran-baran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel