Rayuka 10 sun salwanta yayin da 'yan sanda suka fafata da 'yan daban daji a Katsina

Rayuka 10 sun salwanta yayin da 'yan sanda suka fafata da 'yan daban daji a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ta sanar da cewa ta samu nasarar kasha wasu mutum takwas da ake zargi ‘yan daban daji ne a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Hakan ya fito ne daga bakin babban jami’i mai kula da hulda da al’umma na rundunar ‘yan sandan, Gambo Isah, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a birnin Dikko.

Ya ce a ranar 6 ga watan Agusta, wata tawagar ‘yan sanda ta kai simame kauyen Zamfarawa na karamar hukumar Batsari, bayan samun rahoton cewa ‘yan daban daji fiye da 40 sun kai hari kauyen da bindigu kirar AK 47.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina
Asali: Facebook

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce ‘yan ta’addan sun harbe wani Shafi’i Suleiman mai shekaru 65 da kuma Yakubu Idris mai shekaru 70, baya ga shanu da dama da suka yi awon gaba da su.

A cewarsa, ‘yan ta’addan sun yi wa tawagar jami’an kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa kauyen, inda suka yi gaggawar mayar da martini da har suka samu nasarar kasha daya daga cikin maharani.

Ya kuma ce da dama sun tsere da raunuka na harbin bindiga kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mista Isah ya kara da cewa, tawagar jami’an ta kuma kwato shanu kimanin 30 da ‘yan daban dajin suka sace na al’ummar kauyen.

Haka kuma ya yi bayanin cewa, tawagar ‘yan sandan ta samu naira dubu 23 da alburusai da layu da tulin mabudi daga jikin gawawwakin masu ta’adar.

A wani rahoton Legit.ng ta ruwaito cewa, gudun kada a sake kawo hari ya sa daruruwan jama'a a kudancin jihar Kaduna sun fara tashi daga muhallansu domin neman mafaka a wasu sassan jihar.

KARANTA KUMA: Ku tilasta wa al'umma sanya takunkumin rufe fuska - Buhari ya gargadi gwamnoni

Luka Binniyat, Kakakin kungiyar al'ummar kudancin Kaduna SOKAPU, wanda ya bayyana hakan ya yi alhinin yadda rashin tsaro ke koron al'ummarsa daga mahaifarsu, The Guardian ta ruwaito.

A cewar Binniyat, SOKAPU yanzu na fuskantar kalubalen kula da yan gudun Hijra da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa guduwa daga gidajensu.

Ya ce tun bayan harin daren Laraba, mutanen na tsoron dawowar yan bindigan.

Mutane 33, yawanci yara mata da yara sun rasa rayukansu yayinda yan bindiga dadi suka sake kai hari kauyukan masarautar Atyap dake karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Amma hukumar yan sanda ta ce mutane 21 aka kashe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel