'Yan Najeriya basu fahimci ra'ayin Mamman Daura ba kan tsarin shugabanci - Tsohon Gwamna
Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Babangida Aliyu, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya basu fahimci matsayar Alhaji Mamman Daura ba a kan shugabancin kasar na 2023.
Mamman Daura ya kasance dan uwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Aliyu ya ce a iya fahimtarsa abunda Daura ke kokarin fadi shine cewa duk yankin Najeriya da zai samar da shugaban kasa na gaba, ya kasance cancanta za a duba ba wai yankin kasar da wannan mutumin ya fito ba.
Tsohon gwamnan wanda ya kasance mamba a kwamitin amintattu na PDP, ya bayyana hakan ne a Minna, yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa.
Ya jadadda cewa Najeriya na bukatar mutane kwararru domin kai ta ga matakin ci gaba bayan shekaru 20 da aka kwashe ana rarraba shugabanci ga yankuna.
KU KARANTA KUMA: Hukumar NRC ta yi asarar N1bn saboda dakatar da harkoki
Aliyu ya ce kada a soki Daura “saboda a bayyane yake cewa bayan shekaru 20, tsarin rarraba shugabanci ga yankuna ya gaza haifar da sakamakon da ake muradi.
“Ina ganin Daura na nufin cewa bayan sama da shekaru 20, siyasar kama-kama bai haifarwa da kasar da ‘da mai ido ba, kuma a kan haka, ba wai kawai muna samar da shugaban kasar arewa, shugaban kasar kudu ko kuma Shugaban kasar kudu maso gabas bane.”
Ya kara da cewa “koma wani irin tsari ake dashi, akwai manufar da ake son cimma wa. Bayan sama da shekaru 20 da ake tsarin yankuna, shin kasar ta inganta?
“Muna ta bin shugabancin yanki-yanki tun daga 1999 har zuwa yau saboda muna son hadin kai, kuma muna so kowani yanki na kasar ya ji shima ana yi dashi.
"Muna so Najeriya ta zama tsintsiya madaurinki daya, don haka manufar mika shugabancin kama-kama shine domin kowa ya shiga a dama dashi, amma shin ya bamu abunda muke so?
“A iya fahimta na ina ganin Daura na nufin cewa mun yi shugabancin yanki-yanki sau uku, me zai hana mu duba wani abu na daban; shin bai kamata mu koma ga mataki na gaba don ganin abunda zai faru ba, saboda idan ka ce lokacina ne, zai hana ka neman wannan abun.
Aliyu ya bayar da shawarar cewa kada a soki furucin Daura kan rabe-raben wa’adin shugabanci saboda “koda an raba shugabanci ga yanki, yawan kuri’un da mutum ya samu a zabe ne ke tasiri, don haka ku bari mutane su yanke shawarar abunda zai faru a 2023. A bari al’umma su yanke hukunci kan abunda suke so da kuma yadda suke son shi.”
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen zabar shugaban kasa da ya cancanta saboda “ba wai tsarin bane ke haifar da shugaban kasa nagartacce illa gaskiyar mutanen.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng