PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC

PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC

Kokarin samun kujerar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ne yasa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya koma jam'iyyar APC.

Shugaban kwamitin yardaddun jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jubrin, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Litinin, jaridar The Nation ta ruwaito.

A ranar Juma'a, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, ya sanar da sauya shekar Dogara zuwa jam'iyyar, jim kadan bayan ganawar tsohon kakakin majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati.

Dogara, wanda ya fito daga jihar Bauchi, ya danganta barin jam'iyyar PDP da yayi da banbancin da aka kasa sasantawa tsakaninsa da Gwamna Bala Mohammed na jihar.

Ya alakanta hakan da wadaka da kudin jihar da gwamnan yake yi, ya ce salon mulkin Mohammed ya ci karo da jam'iyyar PDP baki daya.

Amma kuma, shugaban BoT na PDP, ya ce tsohon kakakin bai taba yin korafi a kan salon shugabanci a jihar ba.

PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC
PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Ya ce, "na sha matukar mamaki bayan da na karanta dalilan da suka sa tsohon kakakin majalisar wakilai Dogara ya bar PDP.

"Na kuma yi mamaki da har Dogara bai bi yadda ya dace ba wurin sasanci a kundun tsarin jam'iyyar kafin ya sauya sheka.

"Na kara shan mamaki idan ina tuna matsayin Dogara na tsohon kakakin majalisar da kuma mamba kwamitin amintattu na PDP.

"A matsayinsa na mamba a BoT, Dogara bai taba yin korafi ba a gareni ko a lokacin da yake jam'iyyar. Ganin dalilan da ya bada, za mu iya cewa yana da wani dalili na daban dai.

"Ina tsammanin tsohon kakakin majalisar yana da wata manufa daban da ta sa ya koma APC. Ina tsammanin kujerar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa yake hange a 2023 a karkashin jam'iyyar APC wanda ya san ba zai taba samu ba a PDP.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya nemi a sa Sarkin Dawaki mai tuta da Chiroman Kano a majalisar masu nadin Sarki

"Ina so in sake tabbatar wa da tsohon kakakin cewa PDP za ta ci gaba da zama ginshiki kuma ba za ta taba rufe kofarta ga wani dan Najeriya ba.

"A matsayina na shugaban BoT, ina kira ga dukkan 'yan jam'iyyar da su kwantar da hankali don za mu ci gaba da taka rawar da ta dace kamar yadda yake kunshe a kudin tsarin mulkin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel