Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi

Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi

- An hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwar Ajimobi wanda aka gudanar a harabar gidansa

- Iyalan mariayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo

- Olaniyan ya jira na dan lokaci bayan an ce makullin na wajen matar marigayin, amma daga bisani ya wuce bayan kin bude masa

An sha ‘yar dirama a ranar Lahadi a Oluyole, gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, lokacin da aka hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwarsa, wanda aka gudanar a harabar gidansa.

Iyalan mariayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo kamar a Zoom, YouTube da Facebook.

Olaniyan ya isa gidan da misalin 11:20 na safe a ayarin motoci biyar. Amma da ya kofar da zai shigar dashi hanyar gidan Ajimobi, sai yan sanda da sauran jamián tsaro suka dakatar da ayarin motocin.

Suka ce lallai sai dai motai mataimakin gwamnan nekadai za a bari ya shiga unguwar don halartan taron.

Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi
Yanzu Yanzu: An hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu’an takwas na Ajimobi Hoto: The Nation
Asali: UGC

Da fari jami’an tsaron gwamnan sun ki amincewa da shawarar amma a lokacin da hayaniyarsu ya yi yawa, sai wani babban dan sanda ya sanya baki sannan suka amince cewa motar mataimakin gwamnan kadai ya shiga.

Amma da suka isa gidan Ajimobi, sai suka kara tarar da kofar a rufe. Hadiman mataimakin gwamnan sun gabatar da ubangidansu amma aka sanar masu da cewar an rufe kofar, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75

Sannan cewa uwargidar Ajimobi ce ke rike da makullin. Olaniyan ya jira inda yake tunanin za a magance lamarin kan lokaci.

Bayan ya jira tsawon mintuna 15 ba tare da wani ci gaba ba sai Olaniyan ya bar gidan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel