Tsaro: Bamu da sauran kwanciyar hankali a majalisar wakilai - Kakakin majalisa

Tsaro: Bamu da sauran kwanciyar hankali a majalisar wakilai - Kakakin majalisa

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya nuna damuwa a kan halin fargaba da mambobin majalisar ke ciki saboda rashin tsaro.

A ranar Talata ne aka balle ofishin Kalu da ke cikin ginin majalisar wakilai tare da birkice kayan da ke cikin ofishin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da aka bar daya daga cikin kofofin ofisoshin a bude.

Babu labarin cewa an dauki wani abu a cikin ofishin, sannan ba a san dalili ko niyyar da yasa aka balle ofishin ba.

Kalu, shugaban kwamitin kafafen yada labarai da hulda da jama'a, ya ce faruwar lamarin ya matukar girgiza shi. Kazalika, ya bayyana cewa ya sanar da ofishin jami'an tsaron majalisar abin da ya faru.

"Ba kankanin abin mamaki banea ce wani ya balle kofar ofishina. Har yanzu mu na bincike a kan dalilin yin hakan.

"Shin wani bayani ake nema ko kuwa an yi hakan ne bisa tunanin za a samu kudi ko kuma a dasa min wata na'urar leken asiri? ban san dalilin ba har yanzu.

"Na tabbata 'yan sanda zasu gudanar da bincikensu saboda wannan abin tsoro ne. Ofishi ne na kwamiti," a cewarsa.

Tsaro: Bamu da sauran kwanciyar hankali a majalisar wakilai - Kakakin majalisa
Ofishin da aka balle a majalisar wakilai
Asali: Facebook

Dan majalisar ya kara da cewa hakan ta faru ne sakamakon hutun da majalisar ta tafi bayan bullar annobar korona.

Kazalika, ya bayyana cewa faruwar lamarin ya kara tabbatar da damuwar da wasu mambobin ke nunawa a kan rashi tsaro a majalisar.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa wasu wadanda ake zargin 'yan daba ne sun balle tare da shiga ofishin dan majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

DUBA WANNAN: Za a cigaba da sallar Juma'a a Masallatan jihar Jigawa

Lamarin ya tada hankalin jama'a don ya bayyana gazawa a tsaron ginin majalisar tarayyar kasar nan.

Ofishin na nan a lamba 1.53 na majalisar wakilan Najeriya da ke ginin majalisar tarayya da ke Three Arms Zone, Abuja.

Baya ga dakarun sojin da ke tsaron ginin majalisar, akwai sama da jami'an tsaro 300 da suka hada da 'yan sanda, jami'an NSCDC, jami'an FRSC da kuma na tsaron farin kaya da ke ginin majalisar.

Duk da haka, rashin tsaro, fashi da makami, sata, balle ofisoshi da sauran laifuka sun ci gaba da faruwa a ginin majalisar. Ba sau daya ba ko sau biyu ba, ana samun satar motoci, batiran motoci da kuma sata a shagunan da ke farfajiyar ginin majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel