COVID-19: Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar cewa za a raba wa 'yan Najeriya N30,000

COVID-19: Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar cewa za a raba wa 'yan Najeriya N30,000

- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karyata rahoton da ke bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ba wa 'yan kasa N30,000

- Kamar yadda Femi Adesina ya bayyana, rahoton an danganta shi da shi ne amma bashi da tushe balle makama

- A cewar rahoton bogin, gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin naira don tallafawa miliyoyin 'yan Najeriya saboda muguwar cutar coronavirus

Fadar shugaban kasa ta karyata rahoton da ke ta yawo a yanar gizo mai bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin ba wa duk dan Najeriya da ke da BVN N30,000.

An danganta rahoton da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, Femi Adesina.

COVID-19: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan ba wa kowanne dan kasa N30,000
COVID-19: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan ba wa kowanne dan kasa N30,000
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Tuni kuwa Adesina ya karyata labarin sannan ya ce mara tushe ne balle makama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: "Masu shirya labaran bogi a yanar gizo sun bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kowanne dan Najeriya mai BVN N30,000 don taimaka musu wajen siyen abubuwan bukata kafin a rufe hanyoyin shige da fice a kasar. Wannan ba daga ni yake ba, ba ni na sanar ba."

Kamar yadda rahoton bogin ya bayyana, gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin nairori don taimakawa 'yan Najeriya miliyan 40 da N30,000 kowanne.

Wannan tallafin a cewar rahoton bogin, hakan zai taimakawa 'yan Najeriya masu karamin karfi sakamakon illar da muguwar cutar Coronavirus tayi wa kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel