Ban taba magana a kan Gwamnatin Ganduje da Mukarrabansa ba – Inji Khadijah Sanusi

Ban taba magana a kan Gwamnatin Ganduje da Mukarrabansa ba – Inji Khadijah Sanusi

Yayin da ake cigaba da magana game da sauke Malam Muhammadu Sanusi II da aka yi daga kujerar Sarkin Birnin Kano, mun tattaro maganganun wasu daga cikin ‘Ya ‘yansa.

Da farko dai Khadijah Yusrah Sanusi ta yi karin haske inda ta bayyana cewa tun da ta ke, ba ta taba fitowa ta yi magana game da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ba.

Haka zalika tsohuwar Gimbiyar ta ce ba ta taba cewa uffan game Hadimai da Magoya bayan gwamnan jihar ba. A makon nan ne dai Dr. Abdullahi Ganduje ya tsige Mahaifinta.

Yusrah Sanusi ta yi wannan jawabi ne a kan shafinta na Tuwita, jim kadan bayan gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar tunbuke Muhammadu Sanusi II daga kujerar Sarki.

A ranar da za a tsige Malam Sanusi II daga gadon sarauta, Yusrah Sanusi ta hakaito wata magana da Mahaifin na ta ya taba yi a baya. Shafin ta na Tuwita ya tabbatar mana da haka.

Yusrah ta yi wannan magana ne da karfe 1:00 na safiyar ranar da aka sauke Muhammadu Sanusi II daga mulki. Dubunnan mutane sun yi ta yada maganar Gimbiyar a lokacin.

KU KARANTA: Atedo Peterside ya ji haushin tunbuke Sanusi II da aka yi

“Za ku iya dakatar da ni, amma ba za ku iya dakatar da gaskiya ba. Mutumin da ya yi mani tarbiya, bai taba jin tsoron mulki ya kubce masa domin tsira da mutuncinsa ba.”

Legit.ng ta na kyautata zaton wadannan ne kalaman da tsohon Sarkin ya taba fada a lokacin da Goodluck Jonathan ya tsige sa daga kujerar gwamnan babban banki a 2014.

Shi ma ‘Danuwanta Adam Sanusi watau Ashraf ya yi magana a shafinsa na Tuwita da Instagram, ya na mai godewa addu’o’in jama’a tare da bada hakuri na jinkirin maida martani.

Ya ce: “Na gode maku duka da addu’o’inku, ko da ba haka aka so ba, wannan jarrabawa ce da ba za ta yi masifar wahalar tsallakewa ba idan Allah ya so. Mun gode da goyon baya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel