Obasanjo @ 83: Atiku Abubakar ya koda tsohon Mai gidansa na kin karawa

Obasanjo @ 83: Atiku Abubakar ya koda tsohon Mai gidansa na kin karawa

Yayin da tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ke cika shekaru 83 a Duniya, mataimakinsa, Atiku Abubakar, ya aika masa sakon gaisuwa ta musamman.

Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya na cewa Najeriya ta na bin Olusegun Obasanjo bashi na irin dawainiyar da ya yi mata. Obasanjo tsojon Soja ne wanda ya mulki Najeriya.

Jawabin Atiku ya ke cewa: “Idan aka bayyana ka a matsayin shakundum din siyasar Najeriya, wanda ka ke bin kasa bashi na irin hidimar da ka yi mata, ba a zuzuta ka ba.”

“Mafi yawan mutane za su karanta wannan sakon taya ka murnar ranar zagayowar haihuwarka ne a wayoyinsu na salula, wanda ta na cikin tarihin da ka bar wa ‘Yan Najeriya.”

“Yayin da ka cika shekaru 83 (a Ranar 5 ga Maris), ni da Iyalina mu na taya ka murna da Ubangiji ya ba ka wannan dama.” A gobe Alhamis ne Obasanjo zai cika shekaru 83 a ban kasa.

KU KARANTA: Buhari ya taya Obasanjo murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Obasanjo @ 83: Atiku Abubakar ya koda tsohon Mai gidansa na kin karawa
Atiku ya taya tsohon Shugaba Obasanjo murnar zagayowar ranar haihiuwarsa
Asali: UGC

“Babu ‘Dan Najeriyan da ke tafiya a ban kasa ko wanda ya rasu da ya kawo cigaba a siyasarmu kamar yadda ka kawo mana a lokacin yaki da zaman lafiya, dadi da rashin dadi.”

“Daga kasar Kongo, Afrika ta Kudu, zuwa Angola, da Laberiya, da kasar São Tomé and Príncipe, babu inda tambarin siyasar ka ba ta ratsa ba a kaf Nahiyar Afrika.” Inji Atiku.

‘Dan takarar shugaban Najeriyar a zaben da ya gabata ya fadawa Obasanjo cewa: “Ka yi an gani kuma har yau ka na cigaba da yi wa damakaradiyya hidima da tsare dokar kasa.”

“Ka na bin Najeriya bashin da ba za mu iya biyan ka ba, domin kai ka jagoranci biyan bashin da ba mu taba tunanin biyansa ba. Da wannan kawai, ka ceci al'umma masu zuwa.”

Atiku Abubakar ya ce tsohon Ubangidansa Obasanjo shi ne Mutum na farko da ya fara mika mulki a Najeriya, sannan kuma bayan shekaru 21 ya sake karbar mulki a farar hula.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel