An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika

An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika

- Jennifer Gate, diyar hamshakin mai kudin nan na duniya za ta angwance da masoyinta dan asalin kasar Egypt

- Masoyan junan sun dau a kalla shekaru hudu suna soyayya kafin daga bisani sun yanke shawarar auren juna

- Nasel Nassar dai babban miloniya ne dan asalin kasar Egypt amma mazaunin kasar Kuwait ne

Diyar Bill Gate, Jennifer Gates za ta angwance nan ba da dadewa ba bayan an sa ranar aurenta da masoyinta dan asalin kasar Egypt mai suna Nayel Nassar, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

Jennifer da Nassar sun dau a kalla shekaru hudu suna soyayya kafin daga baya ya bayyana bukatar aurenta. Masoyan junan kan yi tafiye-tafiye tare, kuma su na wallafa hotunansu a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika
An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika
Asali: Facebook

Jennifer mai shekaru 23 a duniya ta sanar da sa ranarta tare da hamshakin miloniya dan kasar Egypt. Ta rubuta:

KU KARANTA: Na rabu da saurayina, saboda idan mutum yayi yaudara a garinsu mutuwa yake take a wajen

"Nayel Nassar, kai daya ne tamkar da goma. Gaskiya ka shayar dani mamaki mai tarin yawa a ranar karshen makon nan. Na kosa in kare rayuwata ina koyo, girma, farin ciki da soyayya tare da kai. Na amince sau miliyan."

A yayin sanar da amincewarta na auren shi, Nayel Nassar ya wallafa "Ta amince!!" A shafin shi. Ya kara da: "Ina ji tamkar nafi kowa sa'a da farin ciki a duniya. Jenn, ke ce duk wani farin ciki na. Na kosa in ci gaba da rayuwa tare da ke da kuma kaunarki. Har abada!"

Cikin kwanakin nan ne Jennifer ta kammala digirinta a jami'ar Stanford. Nayel kuwa wanda ya girma a kasar Kuwait ya yi karatun shi ne a jami'ar Stanford din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel