Haduwar farko: Sarakunan Kano 5 sun nuna 'hamayya' ga juna a wurin taron da Buhari ya halarta

Haduwar farko: Sarakunan Kano 5 sun nuna 'hamayya' ga juna a wurin taron da Buhari ya halarta

- Dukkan sarakunan yanka biyar dake jihar Kano sun hadu a wurin taron da shugaba Buhari ya halarta a Wudil

- Wannan shine karo na farko da sarakunan suka fara haduwa tun bayan da Ganduje ya kirkiri sabbin masarautu a jihar Kano

- Gwamna Ganduje ya kafe a kan cewa ya kirkiri sabbin masarautun ne domin yaduwar cigaba a kowacce kusurwa ta jihar Kano

A karo na farko tun bayan kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano, sabbin sarakunan da aka nada sun share junansu a wurin taron da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarta a karamar hukumar Wudil.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi bakuncin shugaba Buhari yayin ziyarar da ya kai Kano domin halartar bikin yaye wasu dalibai da suka kammala karatu da karbar horo a jami'ar 'yan sanda dake Wudil.

Kafin wannan taro na ranar Alhamis, sabbin sarakunan basu taba haduwa da juna ba tunda gwamna Ganduje ya keta masarautar Kano zuwa gida biyar, kowacce da sarkinta na yanka mai cikakken iko.

Sarakunan sun zauna a jere a sahu na biyu na manyan baki dake bayan wurin zaman shugaban kasa da gwamna.

Yayin da sabbin sarakunan hudu suka zaune a bangaren dama na shugaba Buhari, shi kuwa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya zauna ne shi kadai daga bangaren hagu na sugaba Buhari.

Haduwar farko: Sarakunan Kano 5 sun nuna 'hamayya' ga juna a wurin taron da Buhari ya halarta

Sarakunan Kano 5 sun share juna a wurin taron da Buhari ya halarta
Source: Twitter

Premium Times ta rawaito cewa sarakunan sun share juna, ba tare da sun 'ce ko uffan' ga junansu ba har aka kammala taron kowa ya watse.

Sarki Sanusi ne ya zo wurin taron daga baya, bayan sauran sabbin sarakunan sun jima da zama a a kujerunsu, amma babu wanda a cikinsu ya gaishe shi yayin da yake wuce wa zuwa kujerar da aka tanadar masa.

DUBA WANNAN: 'Yan ta yi dadi ne kawai - Ganduje ya caccaki dattijan Kano dake adawa da kirkirar sabbin masarautu

Kafin kirkirar sabbin masarautun Bichi, Karaye, Gaya da Rano, sarki Sanusi II ne kadai sarki a jihar Kano, lamarin da yasa ya nuna adawarsa ga kirkirarsu.

Da yawan masu nazarin al'amura sun bayyana cewa gwamnatin Kano ta kirkiri sabbin masarautun ne domin rage karfi da ikon sarki Sanusi, saboda sukar gwamnatin Ganduje da yake yi.

Sai dai, a nasa bangaren, Ganduje ya kafe a kan cewa ya kirkiri sabbin masarautun ne domin samun cigaba a kowacce kusurwa ta jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel