Gwamnoni 5 da suka fi shahara a shekarar 2019

Gwamnoni 5 da suka fi shahara a shekarar 2019

Akwai gwamnoni kuma akwai gwamnoni a Najeriya. Wasu gwamnonin ba a jin duriyarsu, wasu kuma suna kan gaba a kafofin yada labarai saboda irin aikinsu. A duk shekara, wasu gwamnonin kan yi zarra saboda wasu dalilai.

A shekarar 2019, wasu gwamnonin sun zama zakarun gwajin dafi. Uku daga cikin zakarun gwajin dafi a cikin gwamnonin, wannan shekarar suka fara hawa karagar mulki yayin da sauran sun kasance a mulki tun shekarun da suka gabata.

A wannan rubutu, Legit.ng ta tattaro muku gwamnoni 5 na Najeriya da suka yi zarra a 2019. Sun hada da:

1. Emeka Ihedioha

Tsohon kakakin majalisar tarayya ne kuma ya hau mulkin jihar Imo a ranar 29 ga watan Mayu. Alamu sun nuna cewa, tsohon dan majalisar tarayyar yana gina jihohin Kudu maso Gabas, yankin da ya sha wuyar rashin shugabanci nagari a shekaru takwas da suka gabata. Duk da hankalinsa ya dauku a farkon hawarsa mulki sakamakon gudumuwar Owelle Rochas Okorocha. Ya mayar da hankali kan shugabancin jihar daga baya. Ya yi suna ne sakamakon fallasar da ya dinga na wadanda suka gabace shi.

2. Seyi Makinde

Dan siyasan mai shekaru 51 Injiniya ne. Makinde ya bayyana cewa duk wani lamarin da ya danganci shugabanci nagari, toh yana da hannu a ciki. Makinde ya fara bayyana kadarorinsa, lamarin da kishiyoyinsa na siyasa suka kasa.

Sabon gwamnan ya koma biyan albashi, ya kashe tsagerun NURTW, ya fara fadada manyan titunan jihar kuma ya zabi matashi mai shekaru 25 a matsayin kwamishina. Wannan ne kuwa ya jawo wa gwamnan suna mai kyau.

3. Bello Matawalle

Dan siyasar mai shekaru 50 na daya daga cikin gwamnoni Arewa da ke haskawa. Gwamnan jam'iyyar PDP din ya fara yaki da 'yan ta'addan da suka gallabi jihar. A yanzu gwamna Matawalle ya yi sasanci da tsagerun kuma sun ajiye makamai tare da rungumar zaman lafiya.

A cikin kwanakin nan ne gwamnan ya datse biyan fansho ga wanda ya gada, lamarin da ya jawo jinjina daga 'yan Najeriya gare shi. Babbar sa'a ce mutanen Zamfara, samun jajirtaccen gwamnan.

DUBA WANNAN: Rikicin fadar shugaban kasa: 'Yan garinsu Buhari sun yi wa Aisha kaca-kaca

4. Godwin Obaseki

Gwamnan jihar Edo ya shiga wannan sahun. Gwamnan ya dau lokaci yana gumurzu ne da wanda ya gada. A maimakon fara shugabanci, ya mayar da hankali wajen yaki da siyasar uban gida. Yakar Oshiomhole ba mummunan lamari bane, ballantana da ya bayyana cewa yaki yake don mayar da hankali don shugabanci nagari.

5. Nasir El-Rufai

Wannan gwamnan shi ake kira da dan baiwa. Masani ne a harkar shuwagabanci kuma sanannnen dan siyasa ne. El-Rufai ya kasance a kanun labarai saboda dalilin rawar da ya taka a siyasar 2019. Daya tarihin da ya kafa a siyasa shine shiga daji da jami'ar tsaro don kama 'yan ta'addan da suka addabi yankin jihar.

Ba a nan ta tsaya ba, daukar mataimakiya mace ya kara wa gwamnan suna. Hatta tsohon shugaban kasa Obasanjo ya jinjinawa tsarin shugabancin gwamnan. Ya kira shi da 'dan baiwa' kuma daya daga cikin mutane masu hazaka da ya yi aiki da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel