Jerin sunayen 'yan Najeriya uku da Amurka ke zargi da damfara

Jerin sunayen 'yan Najeriya uku da Amurka ke zargi da damfara

Kasar Amurka ta mika koke uku da suka hada da damfarar banki, tare da wasu laifuka da wasu ‘yan Najeriya masu suna: Oladayo Oladokun, Farouk Kukoyi da Baldwin Osuji suka aikata. Sun gurafana ne a gaban alkali Robert Lehrburger na wata kotun majistare.

An gurfanar da ‘yan Najeriyan ne tare da wasu mutane 12.

Laifukan da ake zarginsu da shi sun hada da “hada kai da juna tare da amincewa wajen aikata damfara ga banki. Hakan kuwa ya ci karo da sashi na 1344 da 1343 na dokokin Amuraka.”

Wadanda ake zargi da damfarar an gano cewa, sun aikata laifin ne tsakanin watan Afirilu na 2018 zuwa watan Satumba na 2019.

DUBA WANNAN: Kotu ta bada umurnin ajiye jigo a APC a gidan yari kan yi wa gwamnan PDP kazafi

Wadanda ake zargin sun hada kai ne wajen damfarar bankin a matakai kwarara guda uku.

"Sun fara da bude asusun bankuna na kasuwanci sama da 60. An zargi cewa, asusun suna dauke da rijista ne irin na asusun hadin guiwa. Sun kuma bude ne da bayanai da suka hada da sunaye da lambobin tsaro na wasu mutane,” Inji masu gurfanarwar.

“Sun hada kai wajen zuba kudin damfara cikin asusun bankunan, wadanda ake zargi sun samu ne daga damfarar wasu mutane. A wasu wuraren, kudin sata ne.” suka kara da zargin.

“Har zuwa yanzu, hukumomin tsaro sun gano cewa akwai wasu al’amuran damfara wadanda suka hada da damfarar banki har ta $18m." suka kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel