Tashin hankali: Bidiyon yadda wani dafaffen nama ya koma katon maciji

Tashin hankali: Bidiyon yadda wani dafaffen nama ya koma katon maciji

- Wani bidiyo mai cike da abun mamaki da al'ajabi ya cika kafafen sada zumuntar zamani

- Bidiyon na nuna yadda wani dafaffen nama ne ya koma maciji a take gaban mutane

- Tuni jama'ar wajen suka watse don neman tsira da ransu tare da lafiya

Wani bidiyo mai cike da abun al'ajabi ya cika kafafen sada zumuntar zamani. Bidiyon na bayyana yadda wani dafaffen nama ne ya koma maciji a Abraka, jihar Delta.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, naman ya fito ne daga abincin da wani saurayi ya siya wa budurwarshi. Ya siya mata ne a kan hanya yayin da yake komawa gida.

Tashin hankali: Bidiyon yadda wani dafaffen nama ya koma katon maciji

Tashin hankali: Bidiyon yadda wani dafaffen nama ya koma katon maciji
Source: Facebook

A lokacin da naman ya koma macijin, kowa ya ranta a na kare don tseratar da kai. Mutanen da ke wajen sun nemi karyata abinda idonsu ya gane musu. Lamarin ya yi kama da almara.

KU KARANTA: An dauki mutumin da tusar shi ke kashe sauro aiki a wani kamfanin kashe kwari

Duk da cewa, ba a san me ya gudana ba bayan aukuwar lamarin, amma mutane da yawa sun dinga mamakin mene ne sila ko tushen aukuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel