Zaben Kogi: CAN da JNI sun yi Allah-wadai da Jami’an tsaro

Zaben Kogi: CAN da JNI sun yi Allah-wadai da Jami’an tsaro

Daily Trust ta rahoto cewa wasu daga cikin masu ruwa-da-tsaki a harkar zabe, sun nuna rashin gamsuwarsu game da aikin da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su ka yi a zaben jihar Kogi.

Kungiyoyin addini da masu zaman kansu a fadin jihar Kogi, sun koka da yadda ‘yan sanda su ka yi sake a zaben gwamna da kujerar Sanatan Kogi ta yamma tare da sa hannu wajen tafka magudi.

Wadannan masu uwa da makarbiya a kan sha’anin zabe da aka zakulo daga kungiyoyin addinai da jam’iyyun siyasa da sauran masu cin gashin kan-su, sun bayyana haka ne a wajen wani taro.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta INEC ce ta shirya wannan taro a babban birnin jihar Kogi na Lokoja a karshen makon nan. An yi taron ne a Ranar 24 ga Watan Nuwamban 2019.

Rabaren Samuel Owolabi, wanda ya wakilci kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN, ya bayyana zaben da aka yi a matsayin wani yakin basasa, inda ya ce babu aikin da jami’an tsaro su ka yi.

KU KARANTA: Abin da ya sa kotu ta tsare Jagoran jam'iyyar APC a Zamfara

Kungiyar ta CAN ta bakin Samuel Owolabi, ta ce ana ji ana gani aka rika amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a tare da tada-zaune-tsaye a zaben, amma ‘yan sanda su gaza daukar mataki.

Ita ma kungiyar nan ta Jama’atu Nasril Islam ta nuna rashin gamsuwa da kokarin jami’an tsaro a zaben na 16 ga Watan Nuwamba. JNI ta bayyana wannan ne ta bakin Sakataren ta na jihar Kogi.

Isah Ajiboye ya ce hukumar INEC ta yi duk abin da ake bukata na tanadin shiryawa zaben, sai dai jami’an tsaro ne ba su yi kokarin da ya kamata wajen ganin an gudanar da zaben cikin kamala ba.

Bayan Alhaji Isah Ajiboye ya yi jawabi, Mista Nathaniel Abanida, shugaban wata kungiya mai zaman kan-ta, ya soki hukumar INEC a kan kin soke zabe a wuraren da mugun rikici ya barke.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel