Kishi kumallon mata: Budurwa ta kashe kanta bayan ta samu fina-finan batsa a wayar saurayinta

Kishi kumallon mata: Budurwa ta kashe kanta bayan ta samu fina-finan batsa a wayar saurayinta

- Wata budurwa ta kashe kanta, bayan ta samu hotunan batsa a wayar saurayinta

- Budurwar mai suna Lydia Robert ta kashe kanta ne bayan dan rikicin da ya barke tsakaninta da saurayinta, bayan ta nuna rashin jin dadin ta

- Sai dai kuma bayan fitar saurayin nata daga gidan yaje ya dawo, ya dawo ya iske gawar ta har ta kashe kanta

Wata budurwa 'yar shekara 27 mai suna Lydia Roberts, tsananin kishi ya sanya ta kashe kanta bayan ta samu wasu fina-finan batsa a wayar saurayinta, mahaifiyarta mai suna Michelle ce ta bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata.

Lydia na soyayya da wani mutumi dan kasuwa mai suna Adam Wells na tsawon shekara biyu, kafin ta gano wancan abin na cikin wayar shi da ya sanya ta kashe kanta.

A lokacin da saurayin na ta ya fita wajen aiki, Lydia ta ga wasu hotuna a daya wayar shi da ya tafi ya bari a gida, hotunan dai ya dauko su daga wani shafi ne na yanar gizo na kasar Rasha, hakan ya sanya ta kira shi a waya suka fara kace-nace, har zuwa lokacin da ya dawo gida domin ya ci abinci.

KU KARANTA: Bidiyo: An kama wani mai sayar da karas yana wanke karas din da zai sayarwa mutane da ruwan kwata mai datti

Sun cigaba da rikici a cikin gidan, har ya fita ya tafi wajen abokanshi, amma abin mamaki a lokacin da ya dawo gida da misalin karfe 3:30 na dare sai ya iske gawarta har ta kashe kanta, hakan ya saka yayi gaggawar kiran 'yan sanda.

Bayan mutuwar Lydia, an yiwa Wells rijistar shekara biyar a matsayin wanda yake da laifin kallon fina-finan batsa na yara kanana, haka kuma an yanke masa hukuncin yin aiki na tsawon shekara daya ba tare da albashi ba, sannan kuma zai biya kotun majistire dala 85.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel