An kama wani malami yana taimakawa dalibarsa wurin rubuta jarrabawa

An kama wani malami yana taimakawa dalibarsa wurin rubuta jarrabawa

Wani malamin makaranta, Charles Adetunji dan shekaru 40 ya gurfana gaban alkalin kotun Majistare a Ikeja a ranar Alhamis a kan zargin taimakawa wata daliba rubuta jarrabawar ta ta kammala sakandire wato WAEC.

Ana tuhumar Adetunji da ke zaune a gida mai lamba 7 a Oyewole Street, Abule Egba a Legas ta aikata laifuka biyu da suka hada da hadin baki da magudin jarrabawa amma ya musanta aikata laifin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Benson Emuerhi ya shaidawa kotu cewa wanda akayi karar ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba a Meiran Community Junior High School da ke Meiran a Legas.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Emuerhi ya ce wanda aka yi karar ya taimakawa wata matashiya yayin rubuta jarrabawa inda ya tura mata dukkan amsoshin jarabawar Turanci ya aike mata ta wayar salula.

Ya ce, "Mai kula da jarrabawar ya kama dalibar tana amfani da wayan ta, da aka duba sai aka gano amsoshin tambayoyin jarrabawar a ciki; da aka tambaye ta, sai tace wanda aka yi karar ne ya aike mata."

Emuerhi ya ce laifukan sun sabawa sashi na 324 da 411 na dokar masu laifi na jihar Legas na 2015.

Alkalin kotun, Misis Olufunke Sule-Amzat ta bayar da wanda akayi karar beli kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.

Sule-Amzat ta dage cigaba da sauraron shari'a zuwa ranar 5 ga watan Disamba kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel