Yanzu Yanzu: Atiku ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga yan Najeriya, ya sha alwashin samun nasara a kotun koli

Yanzu Yanzu: Atiku ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga yan Najeriya, ya sha alwashin samun nasara a kotun koli

Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairu 2019, Alhaj Atiku Abubakar, ya nuna karfin gwiwar cewa zai samu adalci a karan da ya shigar akan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.

Ya bukaci magoya bayansa da kada su cire tsammani kan cewa za a yi adalci.

Atiku ya yi karar Buhari, INEC da APC bayan bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa, inda ya bukaci a sauya sakamakon da kuma bayyana shi (Atiku) a matsayin wanda ya lashe zabe.

Yayin da yake jawabi a shafinsa na twitter @atiku a ranar Juma’a, 20 ga watan Satumba, tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa cewa:

“Na karbi sakonnin fatan alkhairi masu dumbin yawa daga lungu da sako na Najeriya da kuma dukkan yankuna, addinai da danguna.

“Ina sake mika godiya akan goyon bayanku gareni.

“Har ila yau ina mika godiya ga zababbun gwamnonin jam’iyyana, jam’iyyar Peoples Democratic Party, da kuma kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'yyar kan hadin kai da goyon bayan wannan gwagwarmayar na kotu.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: An nemi wata babbar kwamandar sojin ruwa an rasa a jihar Kaduna

"Koda ace babu abunda mutum zai iya yi don tabbatar da cewar anyi adalci a Najeriya, kawai ka sa a rai cewa hakan zai faru.

"Daga karshe ina son fadin cewa za mu mutu sannan za mu bayar da cikakken bayan akan rayuwarmu a gaban Mahaliccinmu.

“Nagode kuma Allah daukaka Najeriya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel