Ghana za ta koro wasu ‘Yan Najeriya da su buge da karuwanci a Bogo

Ghana za ta koro wasu ‘Yan Najeriya da su buge da karuwanci a Bogo

Hukumar lura da shiga da fice na kasar Ghana ta na shirin dawo da wasu Matan Najeriya, 25, da ta kama su na zaman kan su. Wani babban jami’in hukumar kasar ya bayyanawa ‘yan jarida haka.

Jami’in hukumar shige da ficen da ke kula da shiyyar Bono ta Gabas a kasar Ghana ya tabbatar da cewa za su dawo da ‘Yan kasar Najeriya 25 da su ka kama a Bono ba su da takardun shiga kasar.

Enoch Annor Abrokwa yake cewa da zarar an kammala shirye-shiryen da ake yi, za a tattara wadannan Mata zuwa Najeriya inda su ka fito kamar yadda mu ka samu rahoto daga Daily Trust.

An damke wadannan ‘yan mata ne bayan wani umarni da Ministan yankin kasar, Kofi Amaokohere, ya bada, inda ya nemi jami’ar tsaro su tada duka masu laifin da su ka tare a yankin.

KU KARANTA: An jefi wada da laifin sacewa wani Mutumi mazakuta

Jami’in ya sanar da Manema labarai cewa an yi ram da wadannan masu zaman banza ne a Kudancin Garurwan Nkoranza da Kintampo a lokacin da Ma’aikata su ke wani sinitirin dare.

“Ma’aikatan mu sun kutsa wasu hatsabiban lunguna ne da kimanin karfe 12:00 zuwa 3:00 na dare wata rana inda mu ka kama wasu karuwai kusan 25, dukkansu ‘Yan Najeriya ne.” Inji Jami’in.

Babban Sufirintada Annor Abrokwa ya kara da cewa: “Duk cikin ‘Yan matan babu wani mai alamar shaida irin na zabe, ko fasfon ‘dan kasa.” Annor yace za a fara shirin maida su kasarsu.

A wani bidiyo da aka dauka, an ga ‘yan matan sanye da kananan riguna su na neman kasuwa. An dai ja-kunnen sauran bakin da ke zaune a Yankin Bono da ba su da takardu, su shirya barin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel