‘Yan Shi’an sun yi kicibis da ‘Yan Sanda wajen tattaki Malumfashi

‘Yan Shi’an sun yi kicibis da ‘Yan Sanda wajen tattaki Malumfashi

A yayin da abubuwa da dama ke gudana a yau Ranar Talata, 10 ga Watan Satumban 2019 kuma 10 ga Watan Hijira Muharram, ana bikin Ranar Ashura a wasu bangarori na Duniyar Musulmai.

Mabiya addinin Shi’a su kan nuna takaicinsu game da kisan Imam Husseini a irin yau. A wani bidiyo da ya shigo hannunmu, an ga yadda wasu ‘Yan shi’a su ka ci karo da ‘Yan sanda a Katsina.

A wannan bidiyo na kusan dakika 30 da jaridar nan ta Katsina Post ta wallafa, an ga wasu Mabiya addinin na Shi’a su na tserewa jami’an tsaro yayin da ake jin karan harbin bindigogi su na tashi.

Rahotannin sun bayyana cewa wannan abin ya faru ne a Garin Malumfashi da ke cikin Kudancin jihar Katsina. A wannan fitaccen Gari na Malumfashi akwai dinbin Mabiya addinin na Shi’a.

An hangi wasu Mata cikin bakaken kaya wanda ke nuna alamar shi’anci su na rugowa cikin wani lungu yayin da wasu da-dama su ke tafiya a kan titi inda ake jin jami’an tsaro su na bin su a baya.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Shi'a a Katsina

Har da wani karamin yaro aka gani a wannan bidiyo wanda alamu ke nuna cewa an fatattako sa ne daga inda su ke muzahara. Sauran Mabiya Shi’an da ke yawo su na dauke ne da wata tutar alama.

Har wa yau a wannan bidiyo, an ji wata daga cikin wadannan Mata na Shi’a wanda ke cikin bakaken sutura ta na fadawa ‘yan sandar su zo ayi fito na fito. Kawo yanzu dai ba mu san yadda aka kare ba.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa ba a haramtawa kowa tattaki a fadin kasar ba illa ‘yan kungiyar IMN ta Shi’a. Kwanaki kotu ta tabbatar da kungiyar ta IMN a matsayin ‘yan ta’dda a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel