Shugaban kungiyar Malamai ASUU ya yi ma Sanatoci albishir

Shugaban kungiyar Malamai ASUU ya yi ma Sanatoci albishir

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi ma Sanatocin Najeriya albishirin shan jifa daga wajen yan Najeriya nan bada jimawa ba, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abiodun ya bayyana dalilinsa na yin wannan furuci, inda yace hakan ya zama wajibi sakamakon Sanatocin basa nuna damuwa da matsalolin yan Najeriya, babu abinda suka sani sai matsalar kansu da kansu.

KU KARANTA: Kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin Buhari – fadar shugaban kasa

Farfesan ya yi wannan bayani ne biyo bayan bullara rahoton dake nuna cewa majalisar dattawa ta kammala shirin sayen sabbin motocin alfarma don amfanin Sanatocin Najeriya akan zunzurutun kudi naira biliyan 5 da doriya.

“Suna yawo a cikin motoci masu sulke a daidai lokacin da mutanen da suka wahala a cikin rana da ruwan sama suka bi layi suka zabesu suke cikin halin matsanancin talauci, basu damu da halin da muke ciki bane yasa har suke fada mana zasu sayi motocin alfarma.

“Wannan ai abin haushi ne, ina da tabbacin cewa idan har yan Najeriya suka farga sai sun jefesu da duwatsu, lokaci zai yi da mai kudi bai isa ya yi bacci ba saboda talaka na cikin yunwa, wannan shine abin da shuwagabanni basu ganewa a Najeriya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman a sabon zangon mulkinsa na biyu.

Kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana haka yayin da yake tattauna da gidan talabijin na Channels, inda yace sabuwar gwamnati kadai ake aunawa da kwanaki 100 na farko, hatta a kasar Amurka da Najeriya ta kwaikwayo tsarin bikin rana 100 na farko ba’a auna gwamnatin tazarce da kwanaki 100.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel