Romon Dimokradiyya: An bawa matar Gwamna Matawalle babban sarauta a Zamfara

Romon Dimokradiyya: An bawa matar Gwamna Matawalle babban sarauta a Zamfara

Sarkin Fulanin Zamfara, Muhammadu Chede ya karrama matar gwamnan jihar, Balkisu Bello Matawalle sarautar ta hanyar yi mata nadin saurautar 'Beza'.

Sarkin Fulanin ya sanar da nadin sarautar ne a ranar Juma'a a garin Gusau yayin da Kungiyar Mata Fulani suka kai wa matar gwamnan ziyarar ban girma.

Muhammadu Chede ya yi bayanin cewa, 'Beza' na nufin uwa ga matan fulani a Zamfara.

"Mun nada wa mai girma, Balkisu Bello-Matawalle wannan sarautar ne saboda irin shirye-shirye masu muhimmanci da ta kirkiro da su domin inganta rayuwar matan fulani a jihar.

DUBA WANNAN: Kotu: Ganduje ya gabatar da shaida mai katin zabe na bogi

"Muna murna da irin gudunmawar da gwamnatin Bello Matawallen Maradun ke yi wurin inganta rayuwar fulani a jihar."

A yayin da ya ke mayar da martani, Hajiya Balkisu Matawalle ta yabawa shugabanin fulanin saboda karamcin da suka nuna mata kuma tayi alkawarin cigaba da ayyuka da za su kara dangon zumunci da matan fulani.

"Kamar yadda muka sani, gwamnatin jiha tana shirin kafa Ruga domin makiyaya da kuma makarantu da asibitoci da sauran ababen more rayuwa da suke bukata.

"Ina shirin bullo da wani shiri na musamman na tallafawa matan fulani da ilmantar da su da yaransu baya ga Ruga da gwamnatin jiha za ta kafa," a cewar ta.

A baya, matar shugaban kungiyar fulanin, Aisha Chede ta ce dalilin ziyarar shine neman hadin gwiwa da matar gwamnan kan wasu harkoki da suka shafi mata fulani.

Yayin ganawar, kungiyar ta bawa matar gwamnan kyautan shanu, da nono da wasu kayayakin fulani kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel