Duk da matsalar Boko Haram, NNPC za ta koma tafkin Chadi don hakar man fetir

Duk da matsalar Boko Haram, NNPC za ta koma tafkin Chadi don hakar man fetir

Hukumar albarkatun man fetir na Najeriya, NNPC, ta bayyana aniyarta na sake komawa yankin tafkin Chadi domin cigaba da binciken arzikin danyen mai dake jibge a yankin, kamar yadda shugaban hukumar, Mele Kyari ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kyari ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara zuwa ofishin babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Gabriel Olanisakin, inda ya nemi taimakon rundunar Sojin Najeriya ta wajen samar da tsaro ga ma’aikatansu da kayan aikinsu.

KU KARANTA: Babbar Sallah: Mai Mala Buni ya raba ma zawarawa, marayu da tsofaffi abincin Sallah

Duk da matsalar Boko Haram, NNPC za ta koma tafkin Chadi don hakar man fetir
Duk da matsalar Boko Haram, NNPC za ta koma tafkin Chadi don hakar man fetir
Asali: Facebook

Kaakakin hukumar NNPC, Ndu Ughamadu ya bayyana cewa sakamakon matsalar data dabaibaye yankin tafkin Chadi, NNPC bata samu daman shiga yankin don binciken arzikin mai dake wajen yadda ya kamata ba.

“Na kai ma shugaban hafsoshin tsaron Najeriya ziyara ne don neman taimakon Sojoji wajen sake shiga yankin tafkin Chadi domin mu gudanar da aikin da aka daura mana, muna matukar bukatar taimakonku wajen tsaron ma’aikatanmu da kayan aikinmu.

“Haka zalika muna bukatar Sojoji su dage wajen kare bututun manmu a dukkanin lungu da sakon dake kasar nan, saboda muna samun kalubale daga barayi masu fasa bututun mai.” Inji shi.

A nasa jawabin, ya bayyana NNPC a matsayin wata hukumar gwamnati mai matukar muhimmanci, wanda yace babu shakka zasu bata dukkanin gudunmuwar da take bukata don gudanar da aikinta kamar yadda ya kamata.

Janar Olanisakin ya bayyana wasu ayyuka da Sojoji suke yi don kare bututun mai a Najeriya da suka hada da Operation Wase, da kuma Operation Delta Safe, wanda yace dalilin samar dasu shine kare duk wasu kadarori da kayan aiki da suka shafi mai da iskar gas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel