Wata mata ta datse mazakutar tsohon mijinta ta, ta jefar a masai

Wata mata ta datse mazakutar tsohon mijinta ta, ta jefar a masai

Wata mace da ke birnin Hukou na kasar Taiwan ta datse mazakutar tsohon mijinta da 'yan marainarsa saboda neman mata da ya ke yi a lokacin da suke tare a cewar jami'an 'yan sandan garin.

An ruwaito cewa tsohuwar matarsa, 'yar shekaru 58, Ms Lee ta yi dabara ne ta hanyar motsa sha'awar mijinta a gidansu da ya saki jiki sai da damke mazakutarsa ta sanya almakashi mai kaifi sosai da datse.

Daga nan sai Ms Lee jefa mazakutarsa na tsohon mijinta cikin acid sannan ta zuba cikin masai ta kora da ruwa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashi a Kano

Bayan haka ne mijin mai suna Mr Chen dan shekara 56 ya kira 'yan sanda a waya kamar yadda jami'an tsaro suka bayyana.

'Yan sanda sun tarar da tsaffin ma'auratan biyu a sume a gidan kuma sun garzaya da su asibiti.

'Yan sanda suna jira ma'auratan biyu su farfado saboda su bayar da cikakken bayanin abinda ya faru a rubuce.

Ma'auratan biyu sun raba aurensu ne kimanin wata guda da ya wuce amma Mr Chen ya cigaba da zama gidan tsohuwar matarsa.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa ita ma wata mata a garin Kaduna ta caka wa mijinta ta wuka a ciki.

Matar, mai suna Aisha ta caka wa mijinta mai suna Danasabe wuka a cikinsa. Daga bisani an garzaya da shi asibiti. Sai dai a halin yanzu ba a san dalilin da yasa matar ta aikata hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel