Allah raka taki gona: Na fasa zuwa Saudiyya ne saboda basa goyon bayan 'Yan Madigo da Luwadi - Nicki Minaj

Allah raka taki gona: Na fasa zuwa Saudiyya ne saboda basa goyon bayan 'Yan Madigo da Luwadi - Nicki Minaj

- Fitsararriyar mawakiyar nan Nicki Minaj ta fasa zuwa kasar Saudiyya, bisa wasu dalilai na ta

- Mawakiyar ta bayyana dalilin cewa ita tana goyon bayan kare hakkin masu yin luwadi da madigo ne, inda ita kuma kasar Saudiyya ta haramta hakan

- TUn kafin wannan lokaci da ma kawayenta sun bata shawara akan cewa kada ta kuskura taje kasar Saudiyya wannan wasa

Fitacciyar mawakiyar 'Hip-Hop' dinnan ta kasar Amurka, Nicki Minaj, ta bayyana kudurinta na fasa zuwa kasar Saudiyya kamar yadda kafafen yada labarai a makon da ya gabata.

Nicki Minaj ta bayar da dalilin cewa ta canja shawarar zuwan nata ne, saboda ita tana goyon bayan kungiyoyin da suke kare hakkin masu yin Luwadi da Madigo, yayin da ita kuma kasar Saudiyya ta haramta wadannan abubuwa.

KU KARANTA: Tirkashi: Asirin wani mutumi da 'yan sanda suke nema ruwa ajallo ya tonu, bayan ya saki wata uwar tusa mai firgitarwa

Musulmai da dama sunyi Allah wadai da wannan tsari na gwamnatin kasar Saudiyya, inda suke bayyana cewa bai kamata ace ana irin wannan biki a kasa mai tsarki ba, kasa da ake zuwa aikin Hajji, bayan haka kuma a cikin wannan kasar ne kabarin fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) yake.

Mutanen da suka shirya wannan biki sun bayyana cewa ba za a sayar da giya ko a sha ba har a kammala wannan biki.

A makon da ya gabata ne kasar Saudiyya ta gayyaci fitacciyar mawakiyar Nicki Minaj ne domin ta yi wasa a filin Sarki Abdallah dake birnin Jiddah, ranar 18 ga wannan watan na Yuli da muke ciki.

Wannan gayyata da kasar ta yiwa mawakiyar ta jawo kace-nace a shafukan sada zumunta musamman ga al'ummar musulmi.

Kasar ta Saudiyya ta dauki wannan mataki ne domin kawo canje-canje da zasu jawo hankalin bakin mutane da zasu dinga shigowa kasar domin shakatawa, inda hakan zai kawo wa kasar cigaba ta hanyar habakar tattalin arziki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel