Kotu ta daure wata budurwa shekara 11 a Kurkuku saboda cin mutuncin Ganduje

Kotu ta daure wata budurwa shekara 11 a Kurkuku saboda cin mutuncin Ganduje

Duk tsuntsun daya kira ruwa, shi ruwa ke duka, kamar yadda masu iya magana suke cewa. Anan ma wata budurwace ta kira ma kanta ruwa, kuma a yanzu a iya cewa ruwan ya yi mata duka jagab sharkaf, har ma tana da na sani.

Rahoton jaridar Rariya ya bayyana cewa a kwanakin baya ne wannan budurwa mai suna Ruafidah Ahmad tare da kawarta suka bayyana cikin wani faifan bidiyo suna zagin gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

KU KARANTA: Ba kunya ba tsoron Allah: Tsohon gwamnan APC da matarsa sun kwashe motocin naira biliyan 1

Kotu ta daure wata budurwa shekara 11 a Kurkuku saboda cin mutuncin Ganduje

Rufaidah daga dama
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan matan sun yi ma gwamnan zagin rashin mutunci, zagin rashin da’a, da kuma baje kolin rashin tarbiyya tare da fitsara tsantsa a cikin wannan bidiyo.

Sai dai daga bisani an guda daga cikinsuk, watau Rufaidah Ahmad, inda aka gurfanar da ita a gaban kotun majistri dake lamba 72 a unguwar Nomandsland ta jahar Kano domin ta fuskanci hukuncin laifin da ta aikata.

Inda a ranar Talata, 9 ga watan Yuli ne Alkalin kotun ya yankewa Rufaida Ahmad hukuncin daurin watanni 11 da kuma wata 4 a gidan kurkurku bayan an karanta mata tuhume tuhumen da ake mata, kuma ta amsa da bakinta.

Sai dai abokiyar ta’asar Rufaidah, watau kawarta da suka fito a cikin wannan bidiyo na batanci ga Ganduje ta cika wandonta da iska, inda har yanzu Yansanda ke farautar ruwa a jallo, amma basu shako wuyarta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel