Gwamnatin Bala Mohammed za ta gina Makarantar koyon aikin mai a Alkaleri

Gwamnatin Bala Mohammed za ta gina Makarantar koyon aikin mai a Alkaleri

A cikin makon nan ne mu ka samu labari gwamnatin jihar Bauchi a karkashin gwamna Bala Mohammed za ta bude wata makaranta ta musamman domin karatun abin da ya shafi harkar mai.

Kamar yadda mu ka samu labari daga bakin mai magana a madadin gwamnan jihar na Bauchi watau Dr. Ladan Salihu, wannan makaranta da za a bude za ta taimaka wajen koyawa jama’a sana’a.

Za a gina wannan makaranta ne a cikin Garin Alkaleri da ke karamar hukumar ta Alkalerin jihar Bauchi. Makarantar za ta taimaka wajen samar da kwararru da su ka lakanci aikin man fetur a fadin jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa wannan makaranta da za a bude, za ta samu hadin-gwiwa ne da jami’ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar da kuma wata jami’ar man fetur a Kudu.

KU KARANTA: Mutanen Yobe 700 za su yi Digiri da Digir-gir a kasashen waje

Sabuwar jami’ar man fetur ta tarayya da ke cikin Garin Efferun a jihar Delta za ta taimaka wajen tada wannan makaranta. Salihu ya ce wannan shi ne matsayar da gwamnan ya cin ma bayan taron kwanaki.

Idan ba ku manta ba, a cikin ‘yan kwanakin nan, gwamna Mohammed ya gana da shugaban hukumar TETFund na kasa da kuma shugaban kamfanin man Najeriya na NNPC domin kawowa jihar cigaba.

Yanzu haka gwamnatin tarayya ta na aikin hako man fetur a yankin Bauchi da ke Arewa maso Gabashin kasar. Idan a ka kammala hako man fetur, dole za a nemi kwararru da za su yi aiki a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng