Matashin dan siyasa ya dare mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo

Matashin dan siyasa ya dare mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo

Wani matashin dan siyasa dan shekara 32 mai suna Adebo Ogundoyin dake wakiltar mazabar Ibarapa ta gabas ta jahar Ibadan ya zama sabon kaakakin majalisar dokoki jahar ta tara, ba tare da wata hamayya ba.

Legit.ng ta ruwaito Adebo ya dare wannan mukami ne bayan samun amincewa da kuma goyon bayan kafatanin yayan majalisar dokokin su 32, sakamakon amfani da wasu ma’aunai da yan majalisar suka yi wajen zaben shugabansu.

KU KARANTA: Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9

Matashin dan siyasa ya dare mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo
Adebo
Asali: Facebook

Daga cikin ma’aunan da yan majalisar suka duba wajen zabo Adebo akwai jam’iyyarsa ta PDP, lura da tsarin karba karba, da kuma kasancewarsa guda daga cikin yan majalisu guda hudu da suka sake komawa majalisar bayan lashe zabe a zaben 2019.

Ta amfani da irin wadannan ma’aunai ne majalisar ta zabo dan majalisa Honorabul Ona Ara a matsayin mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo, shima bayan ya samu goyon bayan kafatanin yan majalisun.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman zaben shuwagabannin majalisar akwai sabon gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde, da mataimakinsa Rauf Olaniyan, da kuma sauran jiga jigan sabuwar gwamnatin jahar Oyo.

A wani labarin kuma dadadden dan majalisa dake wakiltar mazabar Ajingi a majalisar dokokin jahar Kano, Honorabul Abdul Aziz Garba Gafasa ya sake zama kaakakin majalisar dokokin jahar Kano a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel