Ya kamata Gwamna Lalong ya sa baki a rikicin Kano – Sarkin Kanam

Ya kamata Gwamna Lalong ya sa baki a rikicin Kano – Sarkin Kanam

Mai martaba Sarkin Kanam da ke cikin karamar hukumar Kanam a jihar Filato, Muhammadu Muazu, ya roki shugaban gwamononin Arewa watau Simon Bako Lalong ya sa baki a rikicin siyasar jihar Kano.

Mai martaba Alhaji Muhammadu Muazu ya roki gwamnan Filato ya sasanta Sarki Muhammadu Sanusi II da kuma gwamna Dr. Abdullahi Ganduje na jihar Kano a matsayinsa na babban gwamnan Arewa.

Sarkin yayi wannan roko ne a lokacin da ya jagoranci wasu al’ummar Musulman kasarsa zuwa gaban gwamna Simon Lalong. Mai martaba Muhammadu Muazu ya kai wa gwamnan ziyarar Idi ne a fadarsa.

KU KARANTA: Mutane 4 da za su sulhunta Sarkin Kano da Gwamna Ganduje

Sarki Muazu yake fadawa Lalong cewa ya kamata Sarakuna da Gwamnoni su hada-kai, su rika aiki tare ne domin kawowa kasa cigaba. Vanguard ta rahoto wannan a Yau Litinin, 10 ga Watan Yuni, 2019.

A wani jawabi da ya fito daga bakin Solomon Gujor wanda shi ne mataimakin Darektan yada labarai na gidan gwamnatin Filato a Jos, Sarkin na Kanam ya roki Gwamnonin Arewa su sulhunta rikicin Kano.

Mai martaban yake cewa idan har aka kashe wutar rikicin da ta kunnu a jihar Kano tsakanin Sarki da Gwamna, jihar za ta cigaba. Mataimakin gwamnan Filato ya godewa Sarkin na Kama da wannan ziyara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel