Umarah: Buhari ya sauka a birnin Madina

Umarah: Buhari ya sauka a birnin Madina

Mun samu cewa a Yammacin yau na Alhamis, 16 ga watan Mayun 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na kasar Saudiya domin gudanar da ibadar Umarah a cikin wannan babban wata na Azumin Ramalana.

Umarah: Buhari ya sauka a birnin Madina
Umarah: Buhari ya sauka a birnin Madina
Asali: Twitter

Ziyarar shugaban kasa Buhari ta yi daidai da amsa goron gayyata na masarautar Saudiya karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdulaziz kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a shafin ta na Twitter a ranar Laraba, ta ce shugaban kasa Buhari zai amsa goron gayyatar Sarki Salman na kasar Saudiya domin aiwatar da aikin Umarah.

KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar da sanadin mai magana da yawun shugaba Buhari, Mallam Garba Shehu, ana sa ran jagoran kasar zai dawo gida Najeriya a ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel