Sojoji sun yi nasarar cafke masu kerawa 'yan ta'adda makamai

Sojoji sun yi nasarar cafke masu kerawa 'yan ta'adda makamai

- Dubun wasu mutane da suke kerawa 'yan bindiga makamai ta cika, inda dakarun rundunar Harbin Kunama III, suka cafke daya a jihar Katsina daya kuma a jihar Neja

- Sojojin sun bayyana cewa kuma sun samu nasarar kwace wasu makamai da suka samu a sansanin 'yan ta'addar a karamar hukumar Kontagora

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarun rundunar Harbin Kunama III, sun kama wani mutumi mai kai wa 'yan bindigar da ke boye tsakanin Jibia da Batsari makamai a jihar Katsina.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojan, Colonel Sagir Musa, ya ce an kama mai kai wa 'yan ta'addar makaman mai suna Marwana Abubakar, wanda aka cafke a kauyen Kwashabawa a cikin karamar hukumar Jibia da ke cikin jihar Katsina, ranar Laraba 8 ga watan Mayu, 2019.

Sojoji sun yi nasarar cafke masu kerawa 'yan ta'adda makamai
Sojoji sun yi nasarar cafke masu kerawa 'yan ta'adda makamai
Source: UGC

Har ila yau, ya ce, dakarun rundunar sojin, sun kai wani hari a sansanin wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a garin Kontagora.

Ya ce a lokacin da suka kai harin sun samu nasarar kwace wasu makamai.

KU KARANTA: Oshiomhole na farauta ta, bayan ni na sa ya zama shugaban jam'iyya - Rochas Okorocha ya koka

Sannan ya kara da cewa sun kuma samu nasarar cafke wani mai kerawa 'yan ta'addar makamai mai suna Salisu Ibrahim, a cikin karamar hukumar Kontagora da ke jihar Neja.

Hakazalika jiya Alhamis rundunar sojin ta bayar da sanarwar cewa ta samu nasarar cafke wasu da ake zargin cewa suna da hannu a sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, wanda ya ke siriki ga babban dogarin Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel